MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Sunan Jami’in Hukumar INEC Dazai Jagoranci Tantance Sakamakon Zaben 2019 Na Shugaban Kasa

       Ni zan jagoranci tantance sakamakon zaben 2019 – Yakubu

A yayin yunkuri da fafutikar tabbatar da gaskiya gami da adalci yayin babban zaben kujerar shugaban kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu na gobe, shugaban hukumar zabe, Farfesa Mahmoud Yakubu ya yi karin haske kan mataki na daurin damarar sa.

Domin tabbatar da tsarki na gaskiya da kuma adalci, Farfesa Yakubu ba tare da wani abokin tarayya ba, ya sha alwashin jagorantar cibiyar kidaya kuri’u da tantance sakamakon zabe a karan kansa domin sauke nauyin da rataya a wuyan sa.

Shugaban hukumar ya kuma bayyana damuwa gami da fargaba ta yunkurin wasu miyagun ‘yan siyasa ma su nufin tayar da zaune tsaye, inda yayi kira ga hukumomin tsaro da su farga wajen kare martabar zaben kasa ta hanyar tsayuwar daka da sauke nauyi da ya rataya a wuyan su bisa tanadi da kuma tsare-tsare na hukumar zabe ta kasa.

Kamar yadda shafin jaridar This Day ya ruwaito, shirye-shiryen hukumar na zuwa ne biyo bayan shawararta ta bayar da dama ga ‘yan jarida da kungiyoyi masu zaman kansu na nan gida Najeriya da kuma kasashen ketare da su kasance cikin harabar cibiyar kidaya kuri’u yayin tantance sakamakon zabe a babban ofishin ta da ke garin Abuja.

Dandalin Mujallarmu ta fahimci, cibiyar kidaya kuri’u ta kasance harabar tattara dukkanin sakamakon zaben shugaban kasa da za a gudanar cikin jihohi 36 da ke fadin kasar nan gabanin bayyana sakamakon zaben. Babban jami’in hukumar ya kuma janyo hankalin al’ummar Najeriya da kuma na kasashen ketare akan kada su sanya wata fargaba ko shakku akan nagarta da ingancin hukumar wajen tabbatar da tsarkakken zabe.

Da ya ke kira kan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, Farfesa Yakubu ya kuma yi gargadin cewa dimokuradiya ba za ta ci gaba da tabbatuwa a fadin kasar nan ba matukar shugabannin da mabiya ba sa yiwa dokoki da’a da biyayya.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-28 — 12:58 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme