KARANTA KAJI: SHUGABA BUHARI YA NADA LAMETEK ADAMU A MATSAYIN SABON MATAIMAKIN BABBAN BANKI NAJERIYA CBN

Ko Miye Dalili? Shugaba Buhari Ya Nada Sabon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya nada sabon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya CBN.

Kamar yadda majiyar ta Dandalin Mujallarmu,keda labari shugaba Buhari yayi amfani da kundin tsarin mulki na kasa sashe na takwas a dokar da aka kaddamar a shekarar 2017.

Shugaba Buhari ya gabatar da Mr Edward Lametek Adamu a gaban majalisar dattawa don tabbatar da dashi a matsayin sabon zababben mataimakin gwamnan bankin CBN na kasa.

Wannan gabatarwar tazo ne acikin wasikar da shugaba Buhari ya aikawa shugaban majalisar ta dattawa Bokula Saraki a ranar 26 ga watan Janairu daya gabata.

Mr Adamu asalin haifaffen dan jihar gombe ne,wanda ya maye gurbin kujerar Suleiman Barau dan garin zaria jihar Kaduna,alokacin da yayi ritaya a watan Disambar shekarar 2007.

Mr Adamu dai ya rike mukaman gwamnati da dama,inda yanzu kuma aka zabe shi a matsayin mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya CBN.

Ko Miye Ra’ayinku Akan Haka?

This website uses cookies.