MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: SHEHIN MALAMI DAN KASAR AUSTRALIA MUHAMMAD TAWHID YA TSALLAKE TARKON WANI DAN DAMFARA A NAJERIYA

Na Tsallake Tarkon Dan Najeriya Da Yayi Kokarin Damfara Ta A Shafin Sada Zumunta Tuwaita-Inji Muhammad Tawhid.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Malamin addinin islama na kasar Australia Iman Muhammad Tawhid ya tsallake tarkon wani dan Najeriya Daya so damfarar sa makudan kudade a shafin sadarwa na zamani tuwaita.

Iman Muhammad Tawhid haifaffen dan kasar Australia ne,asalin dan kasar Iraq,sannan sanannen malami ne dake da dubban masoya dake bibiyar karatuttukan sa a shafukan sada zumunta na zamani a kowace kusurwa a kasashen duniya.

Kamar yadda majiyarmu ta Dandalin Mujallarmu,keda labari kamar yadda Muhammad Tawhid ya wallafa a shafin sa na tuwaita yace wani dan Najeriya yayi kokarin damfarar sa makudan kudade ta hanyar amfani da adireshin sa na Email da ake amfani dashi wajen tura sakonni.

Muhammad Tawhid ya tabbatar da cewa dan Najeriya ya nemi shi daya tura masa dala Amurka $1000 shi kuma dan Najeriya zai turawa  malamin da dala Amurka $ 100,000,000,amma kafin hakan sai shi malamin ya fara turawa da Dala Amurka $1000.

Malamin ya maidawa dan Najeriya da amsa kamar haka,Muhammad Tawhid yace da dan Najeriya daya rage kudin daga cikin dala $1000 da yace zai tura masa ya turo dala $100 kawai ya rike sauran,amma abin mamaki daga lokacin da malamin yace haka sai dan Najeriya yayi shiru mai kara cewa komi ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-02-07 — 12:07 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme