MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: SANATA RABI’U MUSA KWANKWASO YA DAUKI NAUYIN GINA WA ‘YAN GUDUN HIJIRA GIDAJE 350 KYAU TA A BORNO

Za’a fara ginin rukunin gidajen Kwankwasiyya na ýan gudun hijira a Borno

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayi alkawarin gina ma yan gudun hijira dake jihar Borno gidaje guda 350 da kyauta don amfaninsu tare da rage musu radadin halin da suke ciki.
Kwankwaso ya ziyarci jihar ne a ranar Lahadi 24 ga watan Satumba, inda ya kai ziyarar aiki na kwana guda don jajanta ma jama’an jihar bisa bala’in daya afka musu sakamakon rikicin Boko Haram.
Dandalin Mujallarmuta ruwaito Sanatan ya kaddamar da ginin gidaje guda 350 akan hanyar Maiduguri zuwa Gamboru Ngala, wanda yace zai gina ne don amfanin yan gudun hijira, mai suna ‘Kwankwasiyya Model City’.
An gina gidajen ne akan tsarin gida mai dakuna 3. Za’a fara ginin rukunin gidajen Kwankwasiyya na ýan gudun hijira a Borno Kwankwaso yayin isar sa Borno
A wani labarin kuma, Sanatan ya halarci taron saukan Al-Qur’ani na makarantar Darussalam Science and Islamic Academy dake garin Maiduguri.
Filin gidajen Sai dai wasu jama’a sun bayyana ra’ayin cewa manufar ginin wadannan gidaje da tsohon gwamnan jihar Kano Kwankwaso ke yin a da alaka da takarar shugaban kasa daya ke son yi a zaben shekarar 2019.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2017-09-25 — 10:28 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme