MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Sanata Bukola Saraki Ya Bayyana Babban Dalilin Dayasa Dino Melaye Ke Fuskantar Kalubale Hannun Jami’an Gwamnati

Dalilin da yasa Dino Melaye ke dandana kudar sa hannun gwamnatin Buhari – Saraki

Shugaban majalisar dattawan Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Kwara, Sanata Bukola Saraki ya bayyana cewa dalilin da yasa gwamnatin Shugaba Buhari ke ganawa Sanata Dino Melaye azaba shine don ta muzgunawa jam’iyyar PDP da kuma majalisa.

Sanata Saraki ya yi wannan ikirarin ne a yayin da yake jawabi ga dumbin magoya bayan jam’iyyar ta PDP lokacin gangamin yakin neman zaben dan takarar shugabancin kasar Najeriya a tutar PDP Alhaji Atiku Abubakar a garin Jos. Dalilin da yasa Dino Melaye ke dandana kudar sa hannun gwamnatin Buhari

Majiyarmu ta Dandalin Mujallarmu ta kuma samu cewa Saraki din dake zaman shugaban kwamitin gangamin yakin neman zaben Atiku Abubakar din ya kuma bayyana cewa hakan da ake yi masu ba zai taba sa gwuiwoyin su sanyi ba.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a ‘yan kwanakin nan Sanata Dino Melaye ya sha takaddama da jami’an tsaron kasar nan da suka hada da ‘yan sanda da kuma ‘yan sandan farin kaya.

Domin Kallon Sababbin fina finan Hausa Cikin sauka sai kuyi downloading App na Mujallarmu Tv a nan:
Download Mujallarmu TV (284 downloads)

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2019-01-14 — 12:30 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme