MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Sakon Kwankwaso Zuwa Ga Buhari-Abokin Barawo Barawo Ne

Daga hannun Ganduje: Abokin barawo, barawo ne – Sakon Kwankwaso zuwa ga Buhari

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata dake wakiltar mazabar jihar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi tsokaci game da daga hannun Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Shugaba Muhammadu Buhari yayi.

Sanatan wanda ke zaman jagoran darikar tafiyar siyasar nan da ake yi wa lakani da Kwankwasiyya yayi wannan tsokaci ne akan maganar ranar Juma’ar da ta gabata ne a Karamar hukumar Dawakin Tofa lokacin da yake magana a gaban dumbin magoya bayan sa.

Tsohon gwamnan wanda ya nuna rashin jin dadin sa game da daga hannun Gwamnan jihar da Shugaba Buhari yayi, ya kuma fadawa magoya bayan nasa cewa abokin barawo-barawo ne.

Shi dai gwamnan na Kano yana fuskantar matsin lamba ne daga al’ummar jihar tun bayan bullar wasu fayafayan bidiyo dauke da shi yana karbar daloli yana kuma zurawa a cikin babbar rigar sa daga hannun wani dan kwangila.

A wani labarin kuma, Dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf ya ce ya tabbatar tsohon gwamnan jihar Rabi’u Musa Kwankwaso ba zai sa ya yi abin da ba daidai ba.

Da aka tambaye shi, shin idan Kwankwaso ya bukaci ya yi abin da ya saba wa manufofin ci gaban Kano zai bijire masa? Sai ya ce ba bijirewa zai yi ba, zai yi kokarin ganar da shi gaskiya ne ta hanyar bayani.

Ga dai bidiyon nan: 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-02-04 — 9:50 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme