MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: RUNDUNAR SOJAN NIJERIYA TA NADA SABBIN JANAR 29 BIRGEDIYA 95-Duba kaga

     Rundunar Sojan Nijeriya Ta Nada Sabbin Janar 29 Birgediya 95-Karanta kaji

Rundunar sojin Najeriya ta amince da da yin karin girma ga wasu manyan jami’anta zuwa mukaman Manjo Janar, Birgediya janar, da kuma Laftanal Kanal.

A wani jawabi da hukumar ta fitar ta hannun kakakinta, Birgediya Sani Kukasheka Usman, ya nuna cewar an kara wa jami’an soji 29 girma daga mukamin Birgediya janar zuwa Manjo Janar.

Yayin da Kanal 95 su ka samu karin girma zuwa Birgediya janar, sai kuma Manjo guda daya da aka kara wa girma zuwa mukamin Laftanal Kanal.

Wa’anda aka yiwa karin girma zuwa mukamin Laftanal Janar sun hada da Birgediya Janar TOB Ademola, babban jami’in soji a ofishin jakadancin Najeriya a kasar China; Birgediya Janar KO Ogundele, darektan tsare-tsare a hedikwtar tsaro da kwalejin soji; Birgediya Janar ON Ugo; Birgediya Janar AO Uthman; Birgediya Janar M Bashir da Brig Gen MM Mshelia.

Kukasheka Ragowar su ne Birgediya Janar US Mohammed; Birgediya Janar IO Ehiorobo; Birgediya Janar CG Musa; Birgediya Janar CO Ofoche; Birgediya Janar DH Alli-Keffi; Birgediya Janar A Kigbu; Birgediya Janar YI Shalangwa, darektan shari’a na rundunar soji da Birgediya Janar SA Kazaure, darektan hukumar bautar kasa (NYSC).

Sannan ya kara da cewa wadanda aka karawa girma zuwa mukamin Birgediya Janar sun hada da Kananl AA Ayanuga, Kananl SC Ogbuanya, Kananl FO Ilodibia, Kananl EF Oyinlola, Kananl SO Oloyede, Kananl S Kawugana, Kananl FG Dimlong, Kananl OK Falade, Kananl IZ Ohiaka, Kananl CS Okafor, Kananl A Yellow-Duke, Kananl MA Etsu-Ndagi, Kananl AM Alechenu, Kananl Y Yahaya da Kananl IG Lassa. Ragowar sune Kananl PAO Okoye, Kananl AO Oyelade, Kananl MLD Saraso, Kananl VE Emah, Kananl RI Odi, Kananl WD Nasiru, Kananl LA Jimoh, Kananl AP Ahmadu, Kananl QA Ahmed da Kananl JS Sura, da wasu da dama.

An kara wa Laftanal Kanal CA Magaji, AA Bello, CE Ugworji, CY Ufurumazi, K Imam, CE Aniorha, MC Akin-Ojo, KO Kalu, AY Emakoma, MA Dogo, MG Udotong, BA Adeshina da I Sadiq, zuwa mukamin Kanal. Ragowar Laftanal Kanal da aka karawa girma sune NC Achikasim, BI George, YD Ishaku, EA Otseh da SB Salisu, da wasu da dama, sai kuma Manjo UA Musa da aka karawa girma zuwa Laftanal Kanal.

 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-12-05 — 10:13 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme