MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Nnamdi Kanu Ya Bayyana Babban Dalilin Dayasa Ya Gudu Yabar Nijeriya A Shekarar 2017

               Dalilin da ya sa na gudu na bar Najeriya – Nnamdi Kanu

Shugaban kungiyar ‘yan aware ta Biyafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya bayyana cewar ya gudu ya bar Najeriya ne a shekarar 2017 saboda sojoji na yunkurin hallaka shi – Shugaban na IPOB ya zargi Atiku da jawo faduwar Alex Ekwueme a takarar kujerar shugaban kasa da ya yi a shekarar 1999

Kanu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a wani shirin gidan Rediyo da aka yada kai tsaye a London, kasar Ingila Shugaban kungiyar ‘yan aware ta Biyafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya bayyana cewar ya gudu ya bar Najeriya ne a shekarar 2017 saboda sojoji na yunkurin hallaka shi.

“Na gudu ne saboda Buhari ya aika sojoji zuwa gida na domin su kashe ni saboda sun yi tsammanin zan fito domin gwabza fada da su.

Bani da wani makami kamar yadda duk ragowar ‘yan kungiyar IPOB su ke,” a cewar Kanu. Kanu na wadannan kalamai ne a matsayin martini ga ma su goranta ma sa cewar ya gudu ya bar dumbin magoya bayansa a Najeriya.

A cikin hirar, Nnamdi Kanu, ya yi zargin cewar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, dan asalin kasar Kamaru ne.

Akazalika, shugaban na IPOB ya zargi Atiku da jawo faduwar Alex Ekwueme a takarar kujerar shugaban kasa da ya yi a shekarar 1999.

Kanu ya ce: “wasu daga cikin ku ba su san cewar Atiku ne ya yi sanadiyar faduwar Alex Ekwueme a zaben cikin gida na jam’iyyar PDP ba a lokacin da ya fito takara a 1999.”

Shugaban na IPOB ya gargadi ‘yan Najeriya a kan kada kuri’a a zabukan da za a fara cikin wannan watan na Fabrairu. “Yin zabe tamkar kun zabi cigaba da zama cikin kunci da bacin rai ne.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-02-04 — 9:35 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme