KARANTA KAJI: NEYMAR YA ZAYYANA SUNAYEN SHAHARARRUN ‘YAN WASA 3 DA YAKE JINDADIN TAKA LEDA DASU A PSG

Karanta Kaji: Neymar Ya Zayyana Sunayen Mutane Uku Da Yake Jindadin Taka Leda Dasu A Kulob Din PSG.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Shahararren dan kwallon kafa dake taka leda a Kulob din Paris Siant German PSG, Neymar ya bayyana sunayen ‘yan wasa uku daya ke jindadin taka leda dasu a fagen fafatawa a kulob din na PSG.

Kamar yadda majiyarmu ta Dandalin Mujallarmu,keda labari Neymar yace kwata kwata a kulob din na PSG mutane uku ne kacal yake jindadin wasa dasu akokacin da suke taka leda a fili.

Har ila yau Neymar bai tsaya nan har saida ya zayyanu sunayen ‘yan wasan uku daya ce yana jindadin wasu dasu,kamar haka:

Edinson Cavani,Kylian Mbappe,da Angel Di Maria wadannan sune mutane uku da Neymar yace yana jindadin wasu dasu.

1.CAVANI

1.MBAPPE

1.ANGEL DI’MARIA

Neymar ya kara da cewa ‘yan wasa kamar su CAVANI,MBAPPE DA DI MARIA sune yakamata ace kowane kulob ya mallaka,saboda suna da kishin gaske a wajen kwallo.

This website uses cookies.