MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Matar Da Mijinta Ya Saketa Saboda Zaben Buhari Wani Bawan Allah Yayi Alkawarin Aurenta In Tagama Idda

 Idan ta gama idda zan aure ta inji mai neman Matar da ta rasa auren ta saboda Buhari

Kwanan nan ne mu ka ji labarin yadda wani Magidancin ya rabu da Mai dakin sa, a dalilin kurum kaunar shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da ta ke yi,tuni labarin na su dai ya zagaya Duniya.

Soyayyar shugaba Muhammadu Buhari ne ya jawo wannan mata ta rasa auren ta, sai dai kuma, haka-zalika soyayyar da wasu ke yi wa shugaban kasar ya sa wasu kuma su na neman wannan Baiwar Allah da aure yanzu haka.

Wani Bawan Allah ya bayyana cewa a shirye yake ya auri wannan Mata da Mijin ta ya sake ta babu wani dalili illa kurum tana goyon bayan shugaba Buhari.

Zakariyya Abdullahi yace shi zai so ya auri wannnan Baiwar Allah,Buhari Malam Zakariyya Abdullahi yake cewa duk da bai taba ganin wannan Mata ba, amma zai so ya aure ta da zarar ta kammala iddar ta.

Malam Zakariyya ya bada lambar wayar sa domin a tuntube sa a lokacin da ya fara jin labarin ta. Bisa dukkan alamu dai wannan Bawan Allah yana kaunar shugaba Buhari kamar wannan mata don haka yake neman ta zama Mai dakin sa. Soyayyar shugaban kasar ce dai tayi sanadiyyar mutuwar wannan aure a Garin Filato.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-28 — 12:14 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme