MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: LABARIN HALLACIN UWA,RAYUWAR SULTAN DA MAHAIFIYAR SA

Assalamu’alaikum Abokaina Ga wani Sabon Labari Maisuna “HALACCIN UWA”

Marubuci:Haruna Sp Dansadau
LABARIN SULTAN DA MAHAIFIYAR SA.
Sultan dai maraya ne,mahaifinsa ya rasu tun yana cikin mahaifiyar sa.
Bayan haka kuma mahaifan sultan talakawa ne ma zauna wani karamin kauye maisuna kalgo.
Bayan mutuwar mahaifin sultan aka haifi shi.
Watarana mahaifiyar sultan tana cikin damuwa ta yunwa gashi kuma a lokacin sultan bai wuce wata daya da haihuwa ba,saboda haka sai mahaifiyar sultan ta yanke shawara bari tashiga dakin dafa abinci don ta tafasa ruwan zafi ko shayi ta samu ta sha,mahaifiyar sultan tashiga ta aza tukunya akan wuta ta fito waje.
Sai tace bari ta leka kobar gida ko zata samu wani yaro ya taimaka ya amso mata biredi wajen wani mai shago dake kusa dasu ba nisa, ai kuwa mahaifiyar sultan bata samu yaron da zata aika ko daya ba,saboda wannan dalilin shine tace bari taje da kanta.

Mahaifiyar sultan ta dauko hijabin ta ta sanya ta kama hanya zuwa bakin titi da nufin sayen Biredi,sai dai kash!!! Ta manta cewa ta shimfidar da Sultan a daki yana bacci.
Fitar Mahaifiyar Sultan keda wuya sai gobara ta tashi acikin dakin da take dafa ruwan zafi,ma’ana kitchen,sannan kuma dakin yana kusa da dakin da Sultan yake a kwance yana bacci abun sa.
Bayan Mahaifiyar Sultan ta isa wajen mai shago don ta sayi biredi, zuwan ta keda wuya sai taji mutane na ihu suna cewa jama’a ku kawo agaji gobara,Mahaifiyar Sultan ta daga kanta taga inda gobarar take tashi,ai kuwa sai taga ashe gidan su.
Nan take mahaifiyar Sultan ta tuna da cewa ta baro jinjirin dan ta Sultan a daki kwance yana bacci,kuma lallai tabbas idan har wannan wutar tayi karfi toh babu makawa sultan zai iya rasa ran sa.
Mahaifiyar Sultan ba tayi wani bata lokacin ba, ta fasa sayen Biredin da taje saya, ta dawo a guje zuwa gida,tsabar soyayya akan hanya tayi tuntube har sau biyu amma ko a jikin ta,ita dai kawai burin ta ta ceto rayuwar Sultan.
Koda mahaifiyar Sultan ta iso kofar gidan su ta tarar da mutane chunkus a bakin kofa,amma saboda tsabar tsananin zafin wutar babu wani mutum daya da yayi kokarin shiga domin ceto jinjirin yaron ta sultan.
Lokacin da mutane suka hango mahaifiyar Sultan na zuwa, kuma da alama a fusace take,sai sukayi kokarin dakatar da ita daga yunkurin kada tace zata fada cikin gidan,amma ina hakan ya gagara wajen su.
Zuwan mahaifiyar Sultan keda wuya babu ko kwanto ko shawara a zuciyar ta,ta tsunduma cikin gidan,saboda ta ceto rayuwar Sultan ‘Da Cilo guda da Allah ya bata.

Bayan Mahaifiyar Sultan ta shiga cikin gidan ta nufi dakin da Sultan yake aciki,tashiga ta dauko Sultan ta rungume sa a kirjinta.
Alokacin da take kokarin fitowa daga dakin sai wutar ta kara zafi tare da habaka fiye da da, nan take sai wani harshen wuta ya kama gashin kan mahaifiyar Sultan sannan kuma gashi babu wani da zai shigo ya taimaka mata.

Mahaifiyar Sultan tayi iya kokarin don taga gashin kanta ya daina kona,amma ina hakan yaci karfinta, jin shirun da jama’a sukayi saboda kada ayi ba uwa babu ‘da sai aka samu wasu matasa suka shiga cikin gidan.
Shigar Matasan keda wuya sai suka tarar da mahaifiyar Sultan Gashin kanta ya kone sannan kuma fuskar ta a kone,sannan kuma a gefe ga Sultan sai wasan yake abun sa a kirjinta rungume.
Allah sarki wata soyayya sai mahaifiya, sanadiyyar wannan gobara ya nakasa kyan fuskar mahaifiyar Sultan sosai ta yadda kamanninta suka bace daga fuskar ta.

Watarana Mahaifiyar Sultan tana zaune ta rainon Sultan,bayan kwanaki kadan da wucewar faruwar lamarin,sai ta rinka maganar zuci kamar haka.
“Yanzu Shikenan Kamannin Fuska ta sai labari,ko yanzu idan Sultan Ya Girma Zai Yarda Da Cewa Ni Ce Mahaifiyar Sa Kuwa”
Wadannan maganganu sune suke kai da kawo acikin zuciyar mahaifiyar Sultan koda yaushe.

Bayan wasu shekaru Sultan ya Girma sannan kuma Allah ya azurta sa ya zama hamshakin mai kudi,inda daga nan ya koma birni ya gina wasu manyan gidaje tare da sayen wasu motocin alfarma.
Sai Dai Kuma Kash!! A Wata fuskar Sultan yana matukar kyamar kamannin mahaifiyar sa,don so dayawa idan mutane suka tambayesa akan mahaifiyar sa sai yac dasu haka.

“Gaba daya a duniya su basu da wata mummunar mace a zuri’ar su data wuce mahaifiyar sa”
Watarana wadannan kalaman da Sultan yake fadawa mutane da abokan sa,game da mahaifiyar sa sai suka isa zuwa kunnuwan ta.

Lokacin da taji cewa Sultan ke fadin haka,tayi matukar bakin ciki mara misaltuwa, sannan tace wadannan kalamai na Sultan tamkar dai dai suke daya tozarta ta a idan duniya.
Mahaifiyar Sultan ta yanke shawarar zuwa birni ta samu Sultan, ta bashi labarin abinda ya faru shekaru da suka gabata lokacin da yana yaro,sannan da dalilin faruwar wannan konewar dake fuskar ta ta,da ta zama abin kyama a wajen sa.

Sai dai kash!! Ba anan gizo ke sakar ba,bayan Mahaifiyar Sultan ta shiga mota da nufin zuwa birni,a hanyar ta zuwa sai suka samu wani mummunan hadari a hanya,wanda yayi sanadiyyar rasa ranta nan take acikin kankanin lokaci.

Lokacin da labarin mutuwar ta ya riske Sultan, sai yayi matukar nuna farinciki saboda jindadin mutuwar ta.
Awa daya da mutuwar mahaifiyar Sultan kafin a rufe ta,sai ya nufi Kauyen su maisuna “KALGO” inda za’ayi ta’aziyar mahaifiyar ta sa.

Bayan Sultan ya isa kauyen ya shiga ya tarar da mutanen unguwa kowane ransa a bace cike da damuwa tamkar ‘yar uwa su ce ta rasu.
Sultan bai ce da kowa komi ba kawai ya wuce ta gaban su,ya tafi kai tsaye zuwa dakin mahaifiyar sa,saboda yana san ya binciko wasu muhimman takardu.

Bayan Sultan ya shiga dakin mahaifiyar sa yafara bincike,kwatsam sai ya binciko wata ma’ajiyar muhimman abubuwan tarihi na mahaifiyar tare da wani kundin ajiyar bayanai maisuna “DIARY” a harshen turanci da kuma bayani akan mutuwar mahaifin sa.

Ga abinda sultan ya gani rubuce acikin kundin ajiye bayanai kamar haka:
“3 Ga Watan Mayu A Shekarar 1992 An Zabe Ni Amatsayin Sarauniyar Kyawawan Matan Kauyen Kalgo Da Kewaye,Sannan Kuma 14 Ga Watan Junairu Allah Yayi Wa Mijina Alhaji Kamal Rasuwa A Sanadiyyar Hadarin Mota,ya barni da ciki wata shida, Sannan Kuma 2 Ga Watan Ogasta Na Ceto Rayuwar ‘Dana Sultan Daga Cikin Gobarar Wuta,Wanda Shine Yayi Sanadiyyar Rasa Gashin Kaina Da Kyawon Fuskata Da Kowace Mace Take Alfahari Dasu.”

Bayan sultan ya gama karanta wadannan bayanai daya samu acikin wannan kundi na mahaifiyar sa,nan take sai jiri da wata zufa mai makantar da fuska ta sauko masa,inda daga bisani ya fashe da kuka sannan yana mai kallon kansa a matsayin babu wanda yafi asara a duniya..
Yakai dan uwana mai karatu yakamata mu fahimci wani abu guda daya zuwa biyu acikin wannan labari na rayuwar Sultan da mahaifiyar sa.
A rayuwa kada ka taba nuna yatsa ko daga harshen ka akan iyayenka, ko nuna kyamar su a rayuwa,domin su wata kyauta ce da Allah ya bamu saboda watarana zakayi kuka aduk lokacin da basu raye a doron duniyar nan.
Dan Allah Ka Daure Kayi Share da Like,Ko Kayi Comment Da “Ina Sanki Mama” don soyayyar da Kake Yiwa Mahaifiyar Ka.

Daga Naku Haruna Sp Dansadau.
Whatsapp No: 07035169818.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-09-24 — 10:23 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme