MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: KWARARRUN LIKITOCI SUN BAYYANA ILLOLIN DA DUKAN YARA KE HAIFAR A KWAKWALWARSU

Karanta Kaji: illolin Da Dukan Yara Ke Haifarwa A Kwalkwalwar Su-Inji Likitoci

Kwararru sun bayyana cewa dukan yara a matsayin horo yana iya sanya su cikin wani hali,yara suma mutane ne kamar kowa yafi kamata ayi musu magana sama da a dukesu

Duka yana fahimtar da wasu yaran cewa sunyi ba daidai ba yayin da wasu yaran kuma basa ganin hakan Matsaloli da dukan yara ke jawowa a kwakwalwarsu in sun girma, dabi’ar dukan yara a duk sanda sukayi laifi ba abune mai kyau ba.

Kar ku daki yara a lokacin da kuke kokarin nuna musu sunyi ba daidai ba,idan kuma zakayi dukan karkayi shi a lokacin da kake cikin fushi kuma ba tare da daukan wani abun duka ba kamar takalmi ko belt.

Bincike ya bayyana cewa yaran da ake dukansu suna tashi da wata dabi’a sannan kuma basu da wahalar kamuwa da ciwon hauka.

Yara suma mutane ne kamar kowa sunfi bukatar ayi musu magana sama da a dakesu saboda bazasu fahimci dalilin dukan ba wannan yake janyowa su zama masu taurin kai.cewar Dr Adeyinka Labaeka likita a bangaren yara a asibitin University din Ibadan (UCH) jihar Oyo.

Duk da cewa iyaye suna da damar hukunta yara a bisa wani laifi da suka aikata amma akwai horon da bai kamata ayiwa yaro shi ba. A bangaren Dr Abdulmalik kuma yace

” Wasu yaran idan aka dakesu suna fahimtar cewa sunyi ba daidai ba yayin da wasu kuma basa fahimtar hakan suna ganin kawai idan anyi maka abinda bakaso ne kake duka”.

Ya kara da cewa kamar dukan da zai janyo yaro yaji rauni yana zanyo masa cutarwa.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-02 — 11:41 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme