KARANTA KAJI: KOTUN JIHAR DELTA TA YANKE HUKUNCIN KISA GA MUTANE 3 DA SUKA KASHE KAWUN MINISTAN MAI KACHIKWU

AN YAKE HUKUNCIN KISA GA MUTANEN DA SUKA KASHE KAWON MINISTAN MAI KACHIKWU

1/12/2018
Daga Auwal M Kura

Wata Babbar Kotun jahar Delta A Zamanta Da Tayi Ranar Alhamis 11/1/2018 Ta Yankewa Wasu Mutane Su Uku Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Kamusu Da Laifi Kashe Kawon Karamin Ministan Man Fetur a Najeriya Mai Suna Diokpa Felix Boise,

Mutanen Da Aka Yankewa Hukunci dai An Tuhume su Da Laifuka Da Suka Hada Da Kisan Kai Fashi Da Makami ,

Inda Bayan Kamasu Da Laifi Dumu Dumu Alkalin Daya Yanke Hukuncin Justice C.I. Ogisi Ya Zartarwa Mutanen Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Mutanen Da’aka Yankewa Hukunci Sune Kamar Haka Sunday Luka Mai Shekaru (32), Danjuma Kaika Mai Shekaru (37) Da Kuma Luka Agu Mai Shekaru (33),

Ko Kuna Gannin Da Ace Ana Yanke Irin Wannan Hukunci Za’a Cigaba Da Samun Masu Aikata Ta’addanci?

Meye Ra’ayinku

This website uses cookies.