MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: KASHI DAYA CIKIN UKU NA ‘YAN NIJERIYA JAHILAI NE-Inji Ministan Adamu

    Kashi Daya Na ‘Yan Nijeriya Bisa Uku Jahilai Ne-Inji Ministan Ilimi Mallam Adamu

Ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu, ya bayyana cewa yawan jahilai da ba su iya karatu da rubutu ba a Najeriya sun kai kusan miliyan 60, wato kenan a takaice kashi 1 bisa 3 na daukacin mutanen Najeriya duk jahilai ne. Ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu, ya bayyana cewa yawan jahilai da ba su iya karatu da rubutu ba a Najeriya sun kai kusan miliyan 60.

Adamu ya fadi haka ne a jihar Kano, a ranar Laraba, 5 ga wata Disamba inda ya ce wadannan jahilai da ya ke magana a kai, duk matasa ne da kuma magidanta.

Ya ce tunda an kiyasta cewa adadin ‘yan Najeriya sun kai miliyan 180, hakan kenan ya na nufin kashi 1 bisa 3 na daukacin mutanen Najeriya duk jahilai ne kenan.

Ministan wanda ya samu wakilcin Mataimakin Darakta na Fannin Ilimin Firamare da Sakandare, Prince James, ya yi bayanin ne a taron shekara ta 2018 na murnar zagayowar Ranar Ilimi ta Duniya.

Ya kara da cewa kashi 60 bisa 100 na marasa ilimin duk mata ne, yayin da Najeriya ke da yara kanana har miliyan 11 wadanda ke yawo a gari, ba su zuwa makaranta.

Ya ce akwai bukatar a yi gaggawan shawo kan wannan babbar matsala, ganin cewa Najeriya na hankoron cimma kudirin ta na kawar da jahilcin karatu da rubutu da rashin ilimin gaba daya nan da shekara ta 2030.

 

Domin Kallon Sababbin fina finan Hausa Cikin sauka sai kuyi downloading App na Mujallarmu Tv a nan:
Download Mujallarmu TV (2388 downloads)

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-12-07 — 1:15 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme