MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Karshen Magana Nafisa Abdullahi Ta Bayyana Cewa Babu Wata Gaba Tsakaninta Da Jaruma Hadiza Gaborn

  Gaskiyar magana: Babu wata gaba tsakanina da Hadiza Gabon – Nafisa Abdullahi

Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa babu wata gaba tsakaninta da kowanne jarumi ko jaruma a masana’antarsu ta fim Yar wasan fim din Hausan ta yi karin haske kan dangantakarta da jaruma Hadiza Gabo, wadda kowa ya san cewa akwai sabani a tsakaninsu a baya

A shekarar 2017 ne fitattun jaruman biyu suka yi fada inda wasu rahotanni suka ce har da duka yayin da suke tsakar shirya wani fim Nafisa Abdullahi, shahararriyar jarumar fina-finan Hausa, ta bayyana cewa babu wata gaba tsakaninta da kowanne jarumi ko jaruma a masana’antarsu ta fin, tana zaune da kowanne jarumi bisa tsarin da shi jarumin yake so su zauna. Fitacciyar jarumar, ta yi wannan bayanin a cikin wata hira da ta yi da sashen Hausa na BBC a kwanakin baya.

Nafisa ta ce: “Duk wacce ke son zama da ni lafiya lau, to kuwa nima zan zauna da ita lafiya lau, wacce ke da tunani akasin hakan kuwa, to na kan bita da yadda take so.”

Yar wasan fim din Hausan ta yi karin haske kan dangantakarta da jaruma Hadiza Gabo, wadda kowa ya san cewa akwai sabani a tsakaninsu a baya, lamarin da har yanzu wasu ke kallo akwai sauran takun saka tsakanin jaruman biyu. Jarumar ta kuma yi karin haske a kan dangantakarsu da jaruma Hadiza Gabon, wadda suka samu sabani a baya.

Amma da tayi da manema labarai, Nafisa ta ce a yanzu sun fahimci juna ita da Hadiza Gabon bayan da suka dauki dogon lokaci ba sa ga maciji.

Nafisa ta ce, “ko da yake ba mu cika haduwa ba, idan dai har mun hadu muna gaisawa.” Ta ce “dama shi zaman duniya idan dai har ana tare to wata rana dole a samu sabani, domin ko harshe da hakori ma su kan saba.”

A shekarar 2017 ne fitattun jaruman biyu suka yi fada inda wasu rahotanni suka ce har da duka yayin da suke tsakar shirya wani fim.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-26 — 10:20 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme