MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Jarumi Ali Nuhu Ya Cika Shekaru 20 Da Fara Harkar Fim

                        Ali Nuhu ya cika shekaru 20 da fara harkar fim

Ali Nuhu dai ya shiga masana’antar shirya fina-finai a sa’a cikin shekarar 1999 – Tauraronsa na ci gaba da haskawa a masana’antar duk da tsawon shekarun nan da ya dauka yana harkar Shahararren jarumin nan da yaga jiya yaga yau a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu ya cika shekaru 20 da fara harkar fim.

Ali Nuhu dai ya shiga masana’antar shirya fina-finai a sa’a cikin shekarar 1999,jarumin ya samu tarin nasarori kama daga lambar yabo da dama, da kuma tarin daukaka bama a arewacin kasar kawai ba, harma ga sauran sassan kasar dama duniya baki daya.

Tun a zamanin da ya fara fitowa a wasanni tauraronsa ke haskawa inda aka yi ittifakan babu wanda ya kais hi farin jini a masana’antar gabaki daya kama daga wadanda suka fara harkar tare har zuwa ga wadanda ke tasowa a yanzu.

Hakan ya sanya ake yi masa inkiya da sarki mai Kannywood. Sai dai hasashe sun nuna cewa sirrin daukakarsa na daga hazaka da kokarin jarumin akan sana’arsa, sannan kuma shi din mutum ne mai son ganin ci gaban wadanda ke tasowa a masana’antar.

Ya kuma zamo silar shigowar mutane da dama masana’antar, sannan kuma ya zamo silar daukakarsu. Cikin irin wadanna mutane da ya kawo akwai Rahama Sadau wacce tauraronta ke haskawa, da kuma Maryam Yahaya da dai sauransu.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-11 — 1:05 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme