MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Jarumi Adam Zango Ya Bayyana Dalilin Dayasa Yake Wallafa Hotunan Sabuwar Matar Dazai Aura A Kafar Sada Zumunta

Soyayya Ruwan Zuma: Jarumi Adam Zango Ya Bayyana Dalilin Dayasa Yake Wallafa Hotunan Sabuwar Matar Dazai Aura  A Social Media.

Jarumi Adam A.Zango ya fito ya bayyanawa duniya dalilin dayasa yake wallafa hotunan sabuwar budurwarsa mai suna Safiyya wadda ake kira da Sofy.

Tunda ya fara wallafa hotunan nata abin ya zame masa kamar farilla kowane dare sai ya wallafa sabon hoton ta gami da yi mata kalaman soyayya gami da fatan mu kwana lafiya.

Sai dai duk da jarumin na shan maganganu na sukar ra’ayi kan irin abubuwan da suka faru a baya na aure aure da yayi yana rabuwa da matansa hakan baisa yayi kasa a gwiwa ko daina bayyana wannan sabuwar soyayyar tasa ba

Akarshe dai jarumin ya fito ya bayyana dalilinsa na wallafa hotunan na Sofy wanda hakan wani sabon abu ne a tarihin soyayyar jarumin inda mafi yawancin auren nasa ma sai dai aji labari bayan an daura.

Ga Abinda jarumin ya wallafa…..

” Idan ka karfi dukkanin jarabtar da Allah ya kadara maka daga karshe sai yayi maka sakamako mai kyau,nasan cewa duk wanda yaga hoton soffy zaice kyakkyawace

Sai dai kash zuciyarta tafi fuskarta kyau,sannan bana posting hoton matar da zan aura don bakantawa wata ba kamar yadda wasu ke tsammani,ina posting dinta ne don ta kasance mai faranta mi rai tun kafin ta shigo gidana.”

Zuwa yanzu dai jarumin ya wallafa hotunan masoyiyar tasa guda bakwai biyu masu motsi biyar marasa motsi gami da yi mata kalamai na tsantsar soyayya da yabawa halayenta.

 

 

 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-04-01 — 12:46 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme