MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: HUKUMAR NDLEA TA KAMA WANI MUTUM MAISUNA SALISU DAKE SAFARAR MAKAMAI DAGA JIGAWA ZUWA JIHAR BENUWE

Hukumar NDLEA Ta Kama Wani Mutum Maisuna Salisu Dake Kokarin Haurawa Da Makamai Jihar Benue Daga Jigawa.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Jami’an tsaro na hukumar NDLEA sun cafke wani mutum maisuna Salisu dake kokarin haurawa da bindigo zuwa jihar Benue.

Shugaban jami’an tsaro na hukumar NDLEA reshen jihar jigawa masu yakar shige da fice na miyagun kwayoyi Mr Oko Micheal ya bayyana hakane ga manema labarai ajiya talata a garin Dutse jihar Jigawa.

Mr Oko yace sunyi nasarar cafke wannan mai laifi ne alokacin da suka fito aiki suna zagaye gefen gari,inda akan hanyar su ta zuwa kauyen Jahun-Gujungu suka kama Salisu.

Salisu Muhammad an kama shine 4 ga watan Fabrairu ranar lahadi,an same shi da manyan makamai bindigogi da harsasai tare da kananan bindigogi kirar Pistol irin na manyan ma’aikata.

Abisa Rahoton hukumar ta NDLEA tace nan bada jimawa zata tura Salisu Muhammad da kayan laifin da aka kama shi dasu,zuwa babban ofishin ‘yan sanda dake jihar jigawa don cigaba da bincike.

Mai laifin Salisu Muhammad yace shi asalin mutumin jihar Kaduna ne,amma yana karatu a jihar Nasarawa inda daga baya yazama mai safarar makamai daga Nasarawa zuwa jihar Benue.

Salisu Muhammad ya kara da cewa mutane biyu kabilar Tiv da wasu fulani dake zaune a jihar Benue ne suka bashi wannan aiki na sawo masu bindigogi daga wani mutum dake zaune a wani kauyen laraba a jihar kano.

A yanzu haka dai jami’an yan sanda sunyi nasarar kama mutumin daya kira bindigogin daga kauyen na laraba,inda yake tsare a babban ofishin ‘yan dake jigawa tare da Salisu Muhammad.

(Visited 1 times, 1 visits today)
Updated: 2018-02-07 — 1:27 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme