MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Hukumar INEC Ta Gano Tuggun Da Wasu ‘Yan Siyasa Ke Shirya Domin Sayen kuru’u A Lokacin Zabe

Hukumar INEC ta bankado wata sabuwar dabara ta kulla tuggun sayen kuri’u a zaben bana

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC, ta bankado wata sabuwar kitimurmura da ha’incin wasu ‘yan siyasa na kulla tuggun sayen kuri’u a yayin babban zaben kasa na bana ta hanyar amfani da masu sayar da abinci.

Hukumar INEC ta ce a halin yanzu akwai wasu maha’intan ‘yan siyasa da ke shirye-shiryen ribatar masu sayar da abinci a rumfunan zabe wajen kulla tuggu da kuma kisisinar sayen kuri’un zabe a bana.

Jagoran hukumar na kasa, Farfesa Mahmoud Yakubu, shine ya bayar da shaidar hakan a yau Litinin cikin garin Abuja yayin karbar bakuncin tawagar wata kungiyar nahiyyar Turai bisa jagorancin Misis Maria Arena, da za su sanya idanun lura yayin gudanar da zaben kasar nan.

Farfesa Yakubu ya ce bayyanar wannan sabon tuggun wasu ‘yan siyasa na barazana gami da kawo zagon kasa kan ingataccen zabe na gaskiya da adalci da hukumar INEC ta dukufa wajen gudanarwa a kasar nan.

A yayin da nan da kwanaki 25 babban zaben kasar nan zai gudana, hukumar INEC tare da hadin gwiwar masu da ruwa da tsaki ta bankado tuggun wasu ‘yan siyasa na ribatar masu sayar da abinci a rumfunan zabe a matsayin dillalan sayen kuri’u.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, kotu a kasar Senegal ta haramtawa wasu ‘yan takara biyu takarar kujerar shugaban kasa da za a gudanar babban zaben kasa cikin watan Fabrairu na gobe.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-22 — 1:26 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme