MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: DAN KABILAR IBO INYAMURI NE YAYI NASARAR TARWATSA SANSANIN YAN BOKO HARAM A DAJIN SAMBISA-Inji Kashim Shettima

Inyamuri Ne Dan Jihar Imo Yaci Galabar ‘Yan Boko Haram  A Dajin Sambisa-Inji Kashim Shettima.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Gwamnan jihar Borno kashim shettima ya bayyana cewa mutumin da yayi nasarar tarwatsa babban sansanin kungiyar ‘yan boko haram a wanna karon inyamuri ne dan jihar Imo.

Kamar yadda majiyarmu ta Dandalin Mujallarmu,keda labari gwamnan yayi wannan jawabi ne a wajen taron manyan sojoji da kananan jami;an tsaro da aka gudanar a Maiduguri.

Kashim Shettima ya mika jinjina ta musamman ga wanna jami’in soja mai kwazo da yayi abin azo a gani,sannna ya mika godiya zuwa ga gwamnatin tarayyar Najeriya data jajirce tsayin daka wajen ganin ta dawo da zaman lafiya a jihar ta Borno tare da kira ga al’ummar Najeriya da su hada kawunan su wajen bada tasu gudunmuwar don a kauda zalinci da ta’addanci acikin kasa.

Kashim Shettima ya kara da cewa wannan rana ce ta farinciki ga mutanen jihar borno da aka wayi gari yau ‘Yan boko haram basu da wata mafaka da zasu iya boye acikin dajin sambisa gabas yamma kudu da arewa kowace madakata an samu tsaro,bayan shekaru hudu da kananan hukumomin jihar 20 suka kwashe suna fama da matsalar ‘yan ta’adda.

Har ila yau a karshe gwamna Kashim Shettima ya sake mika godiya da jinjina ga wannan inyamuri soja dan garin Mbaise a jihar Imo da yayi nasarar tarwatsa babban sansanin yan boko haram,tare da hadin gwiwar kungiyar sojoji ta Lafia Dole abisa kokarin ta na ganin an kauda boko haram a jihar Borno.

 

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-02-07 — 4:49 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme