MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Dalilin Dayasa Jarumi Adam Zango Kulle Shafinsa Na Instagram Da Kuma Dawowa Jam’iyyar APC Ana Saura Kwana Biyu Zabe

                   Karanta Kaji: Jarumi Adam Zango Yayi Amai Ya Lashe

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Fitaccen jarumin fina finan hausa wanda tauraruwarsa ke haskawa Adam Zango ya kulle shafukansa na sada zumunta wato facebook da Instagram na zuwa wani  lokaci kadan.

Tun bayan lokacin da majiyarmu ta dandalin Mujallarmu.com ta samu labarin ficewar jarumin daga jam’iyyar APC izuwa jam’iyyar PDP,inda jim kadan bayanafkuwar hakan jama’a suka fara cece kuce a shafukan sada zumunta inda jama’a da dama suke zargin cewa jarumin yaje kwadayin dala ne.

Kamar yadda jama’a suka kafa hujja da maganar babba yaron sa wato Nasiru Horo Dan Mama inda akwankin baya ya fitar da wani bidiyo wanda tsawon bai wuce minti biyu ba,inda ya fito fili ya shaidawa duniya cewa shi dai yana nan jam’iyyarsa ta APC daram barin mai gidansa bai zai sa shi canza sheka ba.

Horo dan mama ya kara da cewa yana da tabbacin cewa komai daran dadewa ma gidansa Adam Zango zai dawo jam’iyyar APC,saboda yana da yakinin cewa mai gidan nasa Adam Zango yaje neman kudi ne a jam’iyyar PDP.

Adam Zango dai tun bayan barinsa jam’iyyar APC yake shan suka da zagi ta bangarori daban daban daga ciki har da abokan sa’ar sa na kannywood da ‘yan kallo suma sun tofa albarkacin bakin su game da komawar Adam Zango Jam’iyyar PDP.

Shekaran jiya ne dai jarumin ya fitar da wasu zafafan wakokin APC wa’anda yayiwa suna da ku zabi baba da kuma sai baba inda ya wake shugaba buhari radau da babbar murya,inda wannan ya kara tsuma mutane cikin rudani akan komawar jarumin PDP,shin hakan yana nufin kudi yaje nema amma a zuciyar sa yana APC Sak ne ko yaya?

Sama da mutane biyar sun turawa jarumin sakonni a shafinsa na instagram akan wakokin bidiyon da saki na APC,inda mutane 300 daga cikin dari 500 suka caccaki shi da kuma yin magana ta batanci game dashi akan dawowar sa APC.

Kusan mutane 85 kuma sunyi suka game da zagin Adam Zango,inda kuma sauran mutanen da suka rage dari da sha biyar 115 ne kadai sukayi masa  fatan alkhari.

Majiyarmu ta dandalin mujallarmu.com ta zage damtse wajen ganin ta bincika babban dalilin dayasa jarumin ya kulle shafukan sa na sada zumunta da zuwa hutu na dan wani lokaci amma abin yaki tura

Amma da mu kaji ra’ayoyin jama’a wasu suna cewa Adam Zango sukar da yake sha da caccaka ya shi kulle shafukan sa na instagram ya tafi hutu har zuwa bayan zab,wasu kuma suna ganin cewa duniya ce tayiwa jarumin zafi yasa ya kulle shafukan sa na sada zumunta,inda jama’a da dama daga cikin ‘yan masana’antar kannywood suka rinka sukar sa.

Idan mai karatu bai manta ba kwanakin baya an rinka yada jita jitar cewa ana ganin kamar jarumi Ali Nuhu shine ya  kori jarumi Adam Zango fita daga jam’iyyar APC,bisa la’akari da hasashe da wasu dama suka rinka yi akan cewa daman  jaruman biyu basu ga maciji da juna kaga kuwa ba lallae bane ace su iya tsayawa a tafiya daya.

Wannan dai shine kusan mafi yawan abinda mutane suka rinka zargi kenan a zukatan su bayan jarumi Adam Zango ya canza sheka zuwa jam’iyyar PDP,kawo yanzu dai jarumin bai fidda wani bidiyo ba dake nuna alamun ya dawo jam’iyyar sa ta APC ba,amma jama’a da dama suna ganin cewa bidiyon wakokin baba buhari daya saki kwanan nan su kadai zasu iya gasar da al’umma cewa Adam Zango ya dawo jam’iyyar APC koda kuwa bai ce komai ba.

 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-02-22 — 6:24 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme