MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: DALILAI 6 DAKE SA SAURO CIZON WASU MUTANE

Karanta Kaji Dalilai 6 Dake Sa Sauro Cizon Wasu Mutane. 

Marubuci:Haruna Sp Dansadau. 

Kamar yadda muka sani dai sauro na daga cikin kananan kwari sai dai kuma bala’in sa nada yawa sosai.

 GI

Bisa bincike da wasu  likitoci sukayi sun gano wasu dalilai 6 dake sa sauro cizon wasu mutane.

Ga dalilin kamar haka:-

1-SANYA KAYA MASU DUHU LOKACIN BACCI

hakika sauro wasu lokuta da dama yafi bibiyar mutane dake sanya bakaken kaya ko kuma masu duhu alokacin shiga bacci.

2-YANAYI JINI KO NAU’IN SA

Wasu lokuta sauro yana bin yanayin jinin mutum wata kila nau’in jinin sa mai karfi ne ko kuma mara karfi.

3-NUMFASHI DA KARFI WAJEN BACCI

Su da yawa zaka Samu mutane Idan suna bacci zakaji suna numfashi da karfi wanda hakan na janyo sauro zuwa jikin sune.

4-RASHIN WANKA 

Kamar yadda muka sani waje mara tsafta kamar kwata akoda yaushe baka raba ta da sauro, haka mutum Idan ya zama baya son wanka ko tsaftace toh tabbas akoda yaushe zai zama abincin sauro.

5-MACE MAI CIKI

Sauro yana jindadin shan jinin mace mai ciki, dalilin haka yasa wasu lokuta Idan aka haifi yaro sai a samesa baida lafiya.

6-MUTUM MAI SHAN GIYA

Sauro yana son giya da warin ta sannan kuma yana san jinin da giya ta shiga cikin sa, dalilin haka yasa sauro ke son cizon mutumin dake sham giya.

Allah kara muna lafiya, ya kuma karemu daga cututtuka manya da kanana.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-02-01 — 10:50 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme