MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: BABBAN BANKIN DUNIYA YA GARGADI GWAMNATI BUHARI TAYI TAKA TSANTSAN WAJEN KARBAR BASHI

          Tattalin arziki: Babban bankin Duniya ya gargadi Gwamnatin Buhari

Babban bankin Duniya ta gargadi Gwamnatin Najeriya ta bi sannu a hankali da karbo bashi inda aka nemi a maida hankali wajen jawo hannun jari cikin kasar domin gudun shiga cikin matsala.

Masanan Duniya sun ce akwai hadari idan ba a tsagaita cin bashi ba Bashin da ke kan wasu kasashen Afrikan irin Najeriya ya fara yawa. Sai dai manyan Jami’an Gwamnatin Kasar sun hakikance cewa tattalin kasar bai cikin hadari idan aka duba karfin tattalin Najeriya da kuma nauyin bashin ta.

Najeriya dai ta ci bashin kusan Tiriliyan 6 a cikin shekaru 3 domin cike rarar kasafin kudin kasar a mulkin Shugaba Buhari kamar yadda Jaridar Business Day ta bayyana.

Dalilin haka ne babban bankin Duniya ta ke ganin a sake tunani,babban Jami’in na bankin Duniya na Yankin Afrika Hafez Ghanem ya bayyana cewa a maimakon Najeriya tayi ta cin dan-karen bashi, gara ta jawo ‘Yan kasuwa cikin kasar su gina abubuwan more rayuwa ba tare da an kakabawa mata nauyi ba.

Hafez Ghanem ya kuma nemi Gwamnatin Najeriya ta maida hankali wajen samun kudi shiga ta tatsar haraji da sauran su. Jami’in na babban Bankin Duniya yace dole tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa idan har ana neman ayi yaki da talauci a Kasar. Daga cikin rarar kusan Tiriliyan 2 da ke cikin kasafin Najeriya na bana, ana sa rai za a ci bashin Tiriliyan 1.63 ne wanda akalla Biliyan 800 za su fito daga kasashen waje,babon Mataimakin Shugaban babban bankin Duniyar dai yace akwai gyara.

 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-08-07 — 5:09 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme