MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: AMFANIN CIN FARA SHIDA A JIKIN DAN ADAM

        Karanta Kaji: Amfanin Cin Soyayyar Fara Shida A Jikin Dan Adam

Cin Fara ba sabon abu bane a Najeriya, musamman a yankin Arewacin Najeriya, inda ko a garin Daura da Katsina ana siyar da Fara kwano kwano, kuma ga wadanda suke ci ko suka taba ci, sun tabbatar cewar yana dadi a baki, kuma yana da zaki.

Sai dai dama Hausawa na cewa da magani a gonar yaro, amma bai sani ba, wannan ya sanya Shafin Dandalin Mujallarmu kawo muku jerin amfanin cin fara ga jikin dan Adam, wanda aka gano bayan wani zuzzurfan bincike da masana daga jami’ar Wisconsin-Madison Nelson suka yi.

Soyayen fara Wata mashahuriyar Malama a jami’ar, mai suna Valerie Stull ce ta jagoranci wannan bincike akan Fara, inda tace bincikensu ya nuna akwai mutane biliyan biyu a Duniya dake cin Fara, haka zalika daga cikin amfanin Fara akwai:

Samar da kwayar ‘Probotic’ dake da matukar amfani a jiki

Hana kumburin jiki

Karin jini a jikin dan Adam

Kara karfin garkuwan jiki

Kara karfin kasusuwan jikin dan Adam

Samar da kiste da dumama jikin dan Adam

Taimakawa wajen farfasa abinci a jikin dan Adam

Daga karshe Dakta Valerie ta ce a yanzu haka mutane suka na kara wayewa game da cin Fara, kuma masana sun karkata wajen bincike daban daban akan Fara don gano hanyoyin bunkasa amfaninsa.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-08-06 — 6:38 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme