MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: AISHA BUHARI TAYI KIRA GA MATA ‘YAN SIYASA DAKE JAM’IYYAR APC

Aisha Buhari ta sha alwashin goyon bayan Mata ‘yan takara na jam’iyyar APC

Aisha Buhari, Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta sha alwashi gami da tabbatar da goyon bayan mata ma su sha’awar neman takara karkashin inuwa ta jam’iyyar APC, domin a dama da su cikin harkokin siyasa a kasar nan.

Uwargidan ta shugaban kasa ta bayar da wannan tabbaci ne a ranar Talatar da ta gabata, yayin zababbiyar shugabar Mata ta kasa ta jam’iyyar APC tare da shugabannin jam’iyyar na kowace jiha na kasar nan suka ziyarce ta a fadar shugaban kasa dake birnin tarayya na Abuja.

Kungiyoyin da suka ziyarce ta sun hadar da shugabannin mata na yankin Arewa ta tsakiya, Arewa ta Gabas, Arewa ta Yamma, Kudu ta Gabas, Kudu ta Yamma da kuma na Kudancin Kudu, inda shugabar mata ta kasa ta jam’iyyar APC, Mrs Salamatu Baiwa ta jagorance su.

Aisha Buhari ta sha alwashin goyon bayan Mata ‘yan takara na jam’iyyar APC Hajiya Aisha take cewa, Mata a kasar nan sun bayar da muhimmiyar gudunmuwa tare da taka rawar gani wajen nasarar da zabubbukan da suka gudana cikin kasar nan ta Najeriya a shekarun baya.

Ta ci gaba da cewa, lokaci ya karato da ya kamata a fara damawa da Mata cikin harkokin siyasa tun daga tushe inda kuma ta neme su akan tsayuwar daka wajen da’a ga kundin tsari na jam’iyyar su.

Ta kuma yi kira ga Matan akan su ci gaba da goyon bayan gwamnatin jam’iyyar APC wajen ciyar da kasar nan zuwa ga gaci tare da neman fitowa kwansu da kwarkwata wajen damawa cikin harkokin siyasa.

A na ta jawaban, Hajiya Salamatu ta bayar da tabbacin ta ga uwar gidan shugaban kasa wajen hada kan mata tare da goyon bayan su wajen yi ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar jam’iyyar.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-08-09 — 1:08 am

1 Comment

Add a Comment
 1. *Ni’ima tana bukatar godiya*.
  *Jarabawa. Tana bukatar hakuri*.
  *Zunubi yana bukatar Tuba (Istigfari)*
  .
  *Duk wanda ya yi godiya, ya yi hakuri ya kuma tuba hakika ya samu jin dadi*….
  *Allah ya jiyar damu dadi duniya da lahira*… *BARKAN MU DA SAFIYA.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme