MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Adam A Zango Yazama Jarumi Na Farko Bahaushe Da Yafi Kowane Jarumi Farin Jini A Duniya

Dandalin Kannywood: Adam Zango Yazama Jarumi Bahaushe Na Daya A Duniya Da Yafi Kowane Jarumi Farin Jini-Karanta Kaji

Ajiya  wani fitaccen me bada umarni Mu’azzam Idi Yari yayi wani rubutu daya zama abin muhawara a shafinsa na instagram inda ya bayyana jarumi Adam A.Zango amatsayin wanda kowane jarumi Bahaushe farin jini a duniya.

Ga Abinda Mu’azzam Din Yace….

” Ko Kunsan Adam A.Zango shine tauraro Bahaushe na daya a wajen farin jini a duku duniya,wannan binciken gidan rediyon V.O.A,wato Voice Of America ne  suka binciko a watan daya gabata,wanda bai yarda ba shima ya bincika,,muna tayaka Murna Vasitile Actor Adam A.Zango.”

Adam A.Zango yayi masa godiya inda shima yaje shafinsa ya wallafa wani hoto me rubutu inda shima yake tabbatar da waccan magana ta Director Mu’azzam Idi Yari.

Tabbas duk wani mataki na daukaka jarumi Adam A.Zango ya taka kuma farin jini Masha Allah,dan yana daga cikin jaruman da wasu ‘yan kallo sukan ki sayar faifan video matukar babu hotonsa a jikin bangon faifan kaset din.

Haka zalika yana gaba gaba a jarumai mafiya yawan mabiya a shafukan sada zumunta na zamani muna masa fatan karin cigaba da daukaka gami da tarin masoya da kuma hakuri dasu.

 

Domin Kallon Sababbin fina finan Hausa Cikin sauka sai kuyi downloading App na Mujallarmu Tv a nan:
Download Mujallarmu TV (1487 downloads)

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2019-04-01 — 11:26 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme