MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Abubuwan Al’ajabi Da Jaruma Hadiza Gaborn Tayi Akan Shugaba Buhari Harda Kuka Da Zubar Da Hawaye

 Arewacin Najeriya Aiki Ne Ja A Samu Mace Maison Buhari Kamar Hadiza Gaborn-Inji Jarumi Tijjani Asase.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Siyasa akace rigar ‘yanci,kuma dama shan koko ai daukan rai haka zalika abinda wani keso wani kuma shi yake ki hakanan Allah ya halleci dan Adam, wannan ne dalilin dayasa aka samu rarrabuwar kai a masana’antar kannywood game da zaben buhari da Atiku a zaben 2019.

Masana’antar kannywood ta taka rawar gani matuka a siyasar 2019,domin kuwa duk dan takarar daya samu nasara tsakanin Atiku da buhari,toh lallai akwai gudunmuwar jaruman fina finan Kannywood a nasarar daya samu.

Annan tijjani Asase,wani jarumin fina finan Kannywood ne ya bada shaida akan wata fitacciya kuma mashahuriyar jarumar Kannywood da tauraruwarta ke haskawa,wato Hadiza Gaborn wanda yace tana matukar son shugaba Buhari har hawaye ta taba zubarwa saboda zaben Buhari

Wani ma’abocin kafar sadarwa na zamani facebook,maje El-hajeej Hotoro ne ya bayyana labarin a shafinsa na Facebook,inda yace Tijjani Asase ya tabbatar da soyayyar da Hadiza  keyiwa shugaba Buhari,har yake ganin da wuya a samu kamarta a duk fadin Arewacin Najeriya.

“..Ni na shaida a arewan nan tamu samun mace mai son Buhari kamar Hadiza aiki ne ja,zaben Buhari na farko muna kasar Nijar muna aiki Hadiza tace wallahi saita dawo Najeriya ta zabi Baba.

Alokacin an rufe Boda hankalinta ya tashi harda kuka tayi,wallahi har sai da aka samu ma’aikatan na can dana nan da kyar aka barta ta shigo kasar nan,kuma baza ka taba ganinta a wajen da akeyi da Buhari ba,Inji shi.

Daga karshe Tijjani Asase ya karkare shaidar Hadiza gaborn inda yake cewa

“Kuma har kudinta take kashewa kan a zabi Buhari,yanzu ma gashi ya kamata tabar kasar nan dan cigabanta amma taki ta tsaya saita zabi Baba,Allah ya saka miki Dije.”

 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-02-22 — 7:17 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme