MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANKAJI KAJI: Abinda Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo Yace Bayan Hatsarin Jirgin Da Yayi

 Da dumin sa: Bayan rikitowa daga jirgi, mataimakin shugaban kasa Osinbajo yayi magana

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi magana a karo na farko yayi magana tun bayan da labarin rikitowarsa daga jirgi ya bazu a kafafen yada labarai inda ya tabbatar da labarin sannan kuma yace yanzu yana lafiya.

Mataimakin shugaban kasar ya kuma kara da cewa tuni yacigaba da aikin yakin neman zaben da ya kudurci bayan aukuwar lamarin sannan kuma ya tabbatar da cewa abun takaicin bai same shi ko wani dan tawagar sa ba.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa mun kawo maku labarin cewa jirgi mai saukar angulu wanda ya dau mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo, Sanata Ojudu, mataimakin shi na musamman da liktan matar shi ya rikito daga sama. Hadarin ya faru ne a garin Kabba, jihar Kogi.

Kamar yadda labari daga babban mataimakin farfesa Osinbajo akan yada labarai, Laolu Akande, ya bayyana, hatsarin ya faru ne da tsakar ranar asabar. Osinbajo da sauran wadanda ke cikin jirgin na nan lafiya lau. Kamar yadda mataimakin nashi na musamman ya fada:

“Jirgin mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ya rikito a garin Kabba amma shi da duk wadanda ke cikin jirgin na lafiya. Yana cigaba da al’amuran shi da ya tsara na yau a jihar Kogi.

” Farfesa Osinbajo dai, shine mataimakin shugaba Buhari tun a 2015, kuma ana sa rai muddin aka zarce zai ci gaba har 2023.

Koda yake wasu na ganin dole a tirsasa masa ajje aiki domin a samu Bola Tinubu ya hau kujera ta biyun, ko bayan anci zabe ko bayan rantsuwa.

 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-02-03 — 9:07 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme