MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARAN KAJI: ‘BARAYI SU 150 SUNYI RANTSUWA DA QUR’ANI SUN DAINA SATA HAR ABADA A WANI KAUYE DAKE JIHAR JIGAWA

‘Barayi Su 150 Sun Tuba Daga Barin Sata Har Abada Tare Da Rantsuwa Da Qur’ani Mai Tsarki  A Jihar Jigawa.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

A wani kauye dake jihar Jigawa maisuna Malamawa akan hanyar zuwa karamar hukumar Kafin Hausa barayi su dari da hamsin 150 sun tuba daga barin sata har abada.

A ranar juma’a nan data gabata an bayyana wasu barayi su 150 a gaban dubban jama’a wadannan barayi sunyi rantsuwa da al’qurni mai tsarki akan cewa sun daina sata har abada.

Ada kafin faruwar haka wadannan barayi sun addabi al’ummar yankin da sace sacen motoci da mashina,awaki da shanaye da dai sauran abubuwan sata a garin na malamawa.

Kamar yadda majiyar ta Dandalin Mujallarmu,keda labari Barayin sunyi rantsuwar cewa bazasu kara daukar kayan kowa ba,saya ko saidawa na kayan sata,idan kuma suka kasa cika alkawarin da suka dauka toh Allah ya nuna isharar sa akan su,saboda al’qur’an ba abin wasa bane,inji barayin.

Wannan mataki da mutanen kauyen malamawa suka dauka ya kawo masu masala da wadannan barayi,saboda sun kwashe sama da shekaru 20 suna fama da matsaloli na barayi a bangaren sace sace.

Wani daga cikin barayin maisuna Dantala yace,ya kwashe kimanin shekaru ashirin 20 yana sata ,sannan acikinta yayi aure kuma yake ciyar da iyalan sa da tufatarwa sannan ya taimakwa danginsa da wani abu,amma yanzu ya gane cewa sata ba  hanya ce mai kyau ba saboda haka ya tuba har abada.

Dantala ya kara da cewa yanzu babbar damuwar sa itace yadda zai dauki nauyin iyalansa bayan kuma baida komi da zai iya fara kasuwanci dashi a hannu,don neman halaliyar sa abisa haka suna neman tallafin gwamnati

Mai garin kauyen malamawa Abdulrazak Hamza yace suna mika godiya gun Allah daya kawo lokacin da suka ga karshen wannan bala’i na barayi daya addabe su tsawon shekaru,sannan kuma ya nemawa barayin afuwar mutanen garin na malamawa,da kuma nema masu taimako na tallafin jarin da zasuyi sana’a daga gwamnatin jihar Jigawa.

Akarshe mai garin yace yanzu basuda wani zato na cewa akwai wani sauran barawo da zai rage a yankin tunda sun riga sunyi rantsuwa da littafin Allah mai tsarki,kuma kowa yasan Qur’ani ba abin wasa bane,inji mai garin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-02-07 — 4:55 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme