MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Kalli kwararren telan Najeriya daya dinka ma shugaban kasar Birtaniya riga (Horuna)

Jama’a da dama sun nuna sha’awarsu ga kwalliyar da shugaban kasa Birtaniya, Theresa May ta yi da wata rigar sama da sanya a yayin ziyarar da ta kawo Najeriya a ranar Laraba, 29 ga watan Agusta.

Sai dai abin da jama’a da dama basu sani ba shine wannan riga an dinka shi ne a Najeriya, a shagon wani matashi da yak ware a harkar dinky, wannan yasa jaridar thecables ta kwakulo wannan matashi mai suna Emmanuel Okoro.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Okoro ya bayyana kansa ne a shafin kafar sadarwar zamani ta Instagram, inda ya bayyana godiyarsa tare da mutunta shi da shugaban Birtaniya ta yi ta hanyar sanya rigar daya dinka mata.

Emmanuel Okoro wanda ya bude kamfanin dinki maisuna Emmy Kasbit a shekarar 2014, yace ya samu damar zama da Theresa a yammcin Laraba, inda suka tattauna batutuwa da dama da suka shafi tallafa ma mata.

A shekarar 2017 ne ya lashe kyautar ‘Fashion Focus Prize’ a jihar Legs, inda ya samu kyautar kudi dala dubu goma sha uku da dari tara ($13,900), sa’annan mataimakiyar bankin Amurka Merril Lynch ta bashi horo akan dabarun kasuwanci.

Shi dai Okoro yana amfani ne da atamfofi wajen dinke dinken kayan mata da maza daga cikin wadanda suka sanya kayan da Okoro ya dinka akwai fitacciyar marubuciya Chimamanda Adichie, shahararrun mawakan Najeriya Flavour da Adekunle Gold.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-08-30 — 6:50 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme