MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

JAMI’AN TSARO SUNYI NASARAR CAFKE FITATCEN JAGORAN MASU GARKUWA DA MUTANE A JIGAWA

Daga Auwal M Kura

Rundunar Yan Sanda Reshan Jahar Jigawa Sunfitar Da Sanarwa Samun Nasara Da Rundunar Tasu Tayi Inda Ta Samu Nasarar Kama Wani Shahararren Mai Garkuwa Da Mutane Wanda Ya Addabi Jahar Mai Suna Buba Wanda Rundunar Tadade Tana Nema.

Mai Magana Da Yawun Rundunar Yan Sanda Jahar JigawaSP Abdul Jinjiri,Shine Ya Bayyana Hakan Ga Manema Labarai Inda Yace, “Wanda Ake Zargin Ya Dade Hukumar Yan Sanda Na Nemanshi Ruwa A Jallo Amma Sai Yanzu Ta Samu Nasarar Cafkeshi “

Jinjiri Ya Kara Da Cewa Shekarar Data Gabata Suka Ayyana Buba Matsayin Wanda Ake Nema Ruwa A Jallo Saboda Yadda Ya Addabi Jahar Da Sace Mutane Tare Da Naiman Miliyoyi Domin Fansa .

Buba Ya Sace Wasu Mutane Guda Biyu A garin Kafin Madaki Dake Cikin Karamar Hukumar Gwaram Dake Jahar Ta Jigawa

Haka Kuma Wanda Ake Zargin Shine Shugaban Tawagar Masu Aikata Ta’addanci A Tsakanin Karamar hukumar Gwaram Da Wasu Yankuna Na Jahar Bauchi

Rundunar Yan Sandan Tayi Nasarar Kamashi Ne Bayan da Wanda Ake Zargin Yayi Garkuwa Da Wani Mutum Tare Da Amsar Naira Milyan Uku Sannan Kuma Ya Kashe Mutumin

Yanzu Haka Dai Rundunar Yan Sanda Jahar tace Da Zarar Ta Kammala Bincike Zata Gurfanar Dashi Gaban Kuliya Bisa Laifin Ta’addanc,Garkuwa Da Mutane,Don Fuskatar Hukunci.

(Visited 1 times, 1 visits today)
Updated: 2018-01-08 — 10:21 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme