MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

INA GOYON BAYAN YAJIN AIKIN DA MALAMAI ZASUYI A KADUNA –Sen Shehu Sani

Daga Auwal m Kura

Biyo Bayan Rikici Da Takaddama Da Yaki Ci Yaki Cinyewa Tare Da Dambatwa Kan Koran Malam Jahar Kaduna Su Kimanin Dubu Ashirin Da Doriya Inda Har Takai Kungiyar Malaman Takasa Ta Yannke Hukuncin Tafiya Yajin Aikin Sai Mama Tagani

Sanata Shehu Sani Daya Daga Cikin Sanatoci Uku Dake Jahar Kuma Shike Wakiltar Kaduna ta Tsakiya Ya Fito Fili Ya Goyi Bayan Kungiyar Malaman Inda Yace

Hakkine Daya Rataya Akan Dukkan Wata Kungiya Data Kare Mutunci Da Martabar Ya’yanta Komi Wuya Komi Dadi

Kamar Yadda Sanata Ya Bayyana A Shafinsa Na Facebook Yace” Wannan Yajin Aiki Da Malaman Makaranta Zasuyi Domin Kare Martabarsu Abun Alfahari ne Kuma Ina Jinjina Musu , Mu Samman Uwar Kungiyar Malaman Ta Kasa N U T Kuma Karawa Dimokuradiya Karfine A Kasar”

A Karshe Sanatan Yayi Kira Da Ya’yan Kungiyar Malaman Da Kada Wani Abu Ya Razana Su Wajen Ganin Sun Tunbuke Duk Wani Mai Mugun Nufi Kansu A Jahar Kaduna

(Visited 1 times, 1 visits today)
Updated: 2018-01-08 — 11:47 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme