MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

INA DA SHEKARA 13 AKAYI MIN AUREN FARI-Inji Jaruma Maryma Babban Yaro

             INA DA SHEKARA 13 AKAYI MIN AUREN FARI-INJI JARUMA MARYAM GIDADO

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Maryam Gidado wacce akafi sani da Maryam Babban yaro ta kasance daya daga cikin mata da suka shahara farfajiyar shirya fina finan hausa wato Kannywood.

Maryam dai ta kasance bazawara domin ta taba yin aure har sau biyu,tayi aurenta na farko a lokacin tana ‘yar shekara 13 a duniya kasancewar al’adar fulani na aurar da yara mata da wuri.

Sannan kuma ta haifi ‘Yarta ta farko tana da shekaru 14 bayan shekara daya da auren ta kenan.

Haka zalika ta sake aure inda anan ne ta haifi ‘Danta na biyu,sannan kuma ta bayyana cewa alokacin da take da cikin ‘Dan nata na biyu ne sai mijin ya gudu ya bar ta.

Jarumar ta kuma bayyana cewa burinta ya cika a yanzu musamman a harkar fim sai dai kawai tana burin Allah ya bata miji nagari tayi aure.

Da Aka Tambayi Jarumar Batun Yadda ‘Yan Fim Suka Dauki Lamarin Aure:-Tace

To,ai mu ba ruwan ido muke yi ba,muna tunanin maza suna ganin mu a fim ne,suna son su aure mu don wata manufa da suke da ita.

Shi yasa muke tsoron auren,ba wai muna tunanin wane mai kudi bane ko marar kudi ba.

Don idan ka auri mai kudi ma zai zaci don kudin sa ka aure shi,gara ka auri talaka idan kudin yazo kuna tare da shi.

Toh yanzu abin ne sai ya zama muna tsoron mazan,suma suna tsoron mu.

             Da Aka Tambayi Jarumar Ko Tana Wani Kasuwanci Baya Ga Harkar Fim,Maryam Tace:-

Eh,ina yin kasuwanci don yanzu ina da wajen gyaran gashi a gidan mu,sannan a makarantar mu ina yin aiki na wucin gadi,kuma ina saro kayan mata ina sayarwa.

Ku Gigaba Da Kasancewar Da Wannan Shafi Na Dandalin Mujallarmu Domin Samun Ingantattun Labarai Daga Nan Gida Najeriya Har Zuwa Kasashen Ketare.

Daga Taskar Umar Mai Sanyi

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-06-12 — 1:20 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme