Hukumar VAIDS zata gudanar da Babban taron masu fada Aji a Jahar Kaduna

Mai daraja Gwamnan jihar Kaduna, malan Nasiru el-rufa’I tare da ministan kudi, mrs. Kemi adeosun zasu tattauna da masu rike da mukaman VAIDS a taron da za’ayi gobe Alhamis daya ga watan mayu na shekarar alif dubiyu da goma sha takwas 1st of march 2018 a jihar Kaduna.
Taron karawa juna sanin na hukumar ta VAIDS zai karbi bakuncin shugaban hukumar karbar haraji ta kasa (FIRS), Mr. Babatunde Fowler, da kuma Wasu daga cikin manyan gwamnatin jihar Kaduna, yan majalissun jihar ta Kaduna dakuma sarakunan gargajiya, ta wani gefen akwai manyan yan kasuwa, kananun yan kasuwa da kuma masu biyan haraji.
Taron karawa juna sanin damasu rike da mukaman zai fadakar da dai – daikun jama’a, kananu da kuma manyan yankasuwa masu zaman kansu, kamfanona, kungiyoyi, masu bada shawara akan karbar haraji, masana’antu, masu sana’o’I dayan wasan kwaikwayon dake fadin jihar Kaduna da mazauna yakin domin cin gajiyar shirin, domin cike gibin dake tsakanin gwamnati da kuma mabiyanta, domin ya kara samun kyakkyawar fahimta da wadanda suke cikin shirin.
VAIDS kirkirar gwamnatin tarayya ce domin karawa masu biyan harajin dake fadin kasar nan kwarin guiwa domin su biya harajinsu tsakanin daya ga watan bakwai na shekarar 2017 da kuma talatin daya ga watan ukku na shekarar 2018. Dukkanin masu ruwa da tsakin dasuka amfana da shirin VAIDS zata kebesu daga shan wahalar biyan haraji mai nauyi. Ta yadda zasu ji dadin samun damar habbaka darajar harajin fiye da wata wata ukku

Dayawa,vaida wata damace ta bunkasa harkar kasuwanci acikin kasarnan, kamar yadda haraji keda muhimmanci ga kasa. Ministan kudi, mr. kemi adeosun, ya bayyana biyan harajin yan nigeria nayau da kullum shine asalin abunda zai bunkasa tattalin arzikin kasa da cigaban kasa.

Kasar ta kasa daidaita harajin yan kasar yadda yakamata zuwaga tsari madaidaici, da kuma arziki zuwaga yan kasar, sannan wannan tsarin hanya ce mai kyau ga gwamnati wurin hada kai da mutane don tattalin arziki mai kyau kamar yadda “kudaden shiga zasu kara bunkasa harkar kasuwancin daga gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jiha da kayayyakin more rayuwa da kirkiro ayyuka da kuma samar da kudade a cikin kasa,”

This website uses cookies.