MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

HUKUMAR KULA DA ALHAZAI DA AIKIN HAJJI TA KARA WA’ADIN BIYAN KUDI ZUWA RANAR….

An Kara Wa’adin Biyan Kudin Hajjin Bana
Basheer Journalist Sharfadi
March 30, 2018 zero comment
Hukumar Alhazai Ta Kara Wa’adin Biyan Kudin Hajjin Bana.

Biyo bayan ganawa da jama’a akan aikin Hajji, hukumar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta kara wa’adin rufe karban kudin maniyyatan aikin hajjin bana wanda dama an sanya 31 ga watan Maris, yanzu kuma an kara zuwa karshen watan Afrilu.
Karin wa’adin ya biyo bayan korafe korafen jama’a inda suka nemi a kara lokaci.
Hukumar Wadda ta fitar da wata takarda zuwa ga manema labarai, dauke da sa hannun Fatima Mustapha, tace zata yi amfani da karin lokacin wajen sanar da hakikanin kudin kujerar zuwa aikin hajjin na wannan shekara, tare da cewa kudaden zasu banbanta bisa ga yanayin jihar da mutum yake.
Hukumar tace tana kira ga maniyyata da su yi kokarin kammala biyan Kudin kujerar kafin karewar wa’adin.
Yanzu haka tawagar hukumar na kasa mai tsarki don kammala shirin sanar da kudin kujeran na bana.

Updated: 2018-03-30 — 4:24 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme