MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

HARE HAREN BIRNIN GWARI YAYI KAMA DANA BOKO HARAM — SANATA SHEHU SANI

Rashin Tsaro Ya Ta’azzara A Jahar Kaduna – Cewar Shehu Sani

Daga Auwal M.Kura

Dan Majalisa Dake Wakiltar Kaduna Ta Tsakiya A Majalisar Dattijan Najeriya Shehu Sani , Ya Bayyana Damuwar Sa Kan Yadda Kashe Kashe Da Garkuwa Da Mutane Ke Kara Ta’azzara A Yankin Birnin Gwari Dake Jahar,
Inda Sanata Yace Yadda Ake Kai Hare Hare A Yankin Bashi Da Banbancin Da Yadda Kungiyar Boko Haram Ke Kai Hare Hare A Arewa Maso Gabashin Najeriya.

Da Yake Mika Rakonsa Ga Majalisa A Ranar Laraba 16/05/2018 ,Shehu Sani Yace” Rahoton Kashe Kashen Da Ake Bawa Gwamnatin Tarraya Bai Kai Yadda Ake Kashe Mutane A Yankin Ba, Don Haka Gwamnatin Tarayya Ya Kamata Ta Dauki Tsatstsauran Mataki Kamar Yadda Ta Dauka Na Boko Haram,”

Shehu Sani, Ya Kara Bayyana Yadda Birnin Gwarin Ke Fuskantar Barazana Ta Kashe Kashe Da Garkuwa Da Mutane,Wanda A Kwanaki Uku Da Suka Wuce An Sace Mutane Tamanin Da Uku Lokaci Daya, Wanda Akayi Garkuwa Dasu.”

A Karshe Sanata Shehu Sani Ya Roki Yan Majalisar Dama Gwamnatin Tarayya Dasu Dauki Duk Wani Mataki Da Zai Tabbatar Da Tsaro Da Kawo Karshen Kashe Kashen Dake Faruwa A Birnim Gwari

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-05-17 — 5:01 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme