MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Har yanzu musulman Arewa na karkashin mulkin mallaka ne – Sarki Sanusi

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

ya yi kira ga gwamnatocin Arewa da
su nemi a rika koyar da ‘Yan Arewa
a jami’o’in yankin da harshen
Hausa.

Sanusi ya bayyana haka ne a wajen
taron kaddamar da wani fim da wata
‘yar kasar jamus mai suna Hannah
Hoechner ta shirya da ke nuna
yadda rayuwar Almajiri ya ke.
Sarki Sanusi ya ce kallon hadarin
kaji da ake wa Almajirai da
Almajiranci a kasar nan ya isa
hakanan.

” A kasar nan an maida idan ka iya
turanci shi kenan, ka zama jarumi
wayayye mai ilimi, ba a ganin idan
za ka iya rubutu da larabci ko
karatu shima ilimi ne ko kuma
shima wayewa ne.

” Bayan kuwa akwai ilimin Arabi
sannan ana rubuta larabci da ajami
ma shekaru 600 kafin zuwan turanci
kasar nan.

” Dole ne fa musulmai su nemi
‘yancin su a kasar nan domin kuwa
har yanzu musulunci na karkashin
mulkin mallaka ne. Saboda ba a
dauki al’adun mu da Harshen mu a
bakin komai ba.

” Idan da za aka karanta littafan
musulunci bila adadin, idan ba
turanci ka iya ba ko ka karanta ba,
ba a daukan ka a bakin komai a
kasar nan.

” Sarkin Kano Muhammadu Rumfa
tun a zamanin da wato tunkafin
zuwan turawa ya kan aika
mutanenzuwa kasar Barni, da
Mauritania domin karatun Islama.
Sarki Sanusi ya kara da cewa a tun
farko wani Rabaren ne mai suna
Miller ya fara rubuta wa Lord
Lugard wasika da a daina amfani da
larabci da ajami a matsayin yaren da
za a rika aiki da shi a Najeriya.

” Ku duba kasashe kamar su Egypt,
China duk da harsunan su suke
karantar da daliban su. Haka kuma
ko a jihar Legas, an kirkiro dokar da
dole sai ka ci darasin na yaren ‘yar
banci sannan za ka samu damar
shiga manyan makarantu mallakar
jihar.

Yayi kira ga gwamnatocin Arewa da
su kirkiro tsarin da zai ba da dama a
rika karantar da ‘yan Arewa da
harshen Hausa.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme