MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

HAMSHAKIN MAI KUDI NA DUNIYA BILL GATE ZAI HALACCI BIKIN DIYAR ALIKO DANGOTE FATIMA-Karanta Kaji

         Hamshakin Mai Kudi Na Duniya Bill Gate Zai Zo Bikin Diyar Dangote Fatima

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Kamar yadda majiyar ta Dandalin Mujallarmu,keda labari shahararren hamshakin mai kudi na duniya Bill gate zai halarci bikin diyar Aliko Dangote Fatima wanda za’ayi anan Najeriya a watan 3 na wannan shekarar.

Kwanan nan ne dai aka sanya ranar bikin na diyar Dangote fatima tare da dan gidan tsohon shugaban yan sanda na kasa MD Abubakar,maisuna Jamil.

Jamil Abukbakar shine ‘Da na farko ga MD Abubakar wanda yayi karatunsa a jami’ar Kingston University dake Ingila,inda ya karanci fannin kwamfuta a bangaren sadarwa na zamani bayan ya kammala shine sai ya nemi aiki a ma’aikatar tukin jirgin sama wato Airwings.

Wannan shagali da za’ayi na ‘ya’yan masu hannu da shuni manyan mutane zasu samu halarta bikin,ciki harda shugabannin kasa hudu daga kasashen waje game da shugaba Buhari cikon na biyar anan Najeriya.

Bill Gate ya kara da cewa yadda alakar sa da Dangote take babu abinda zai iya hana shi  zuwa  wannan bikin na aminin sa hamshakin dan kasuwa na Africa Aliko Dangote a cewar sa.

 

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-02-07 — 10:58 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme