MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

GASKIYA TA BAYYANA: FASTO YA KARYA TA ADDININ KIRISTA SANNAN YA DANGANTA SHI DA TATSUNIYA-Inji Revaren Bempah

Yesu Almasihu Ba Dan Allah bane,Sannan Addinin Kirsita Na Yanzu Kage Ne-Inji Fasto Revaren Bempah

Revaren Bempah ya kawo wata sabuwar fahimta a addinin krista – Bempah ya ce ‘Yeshua HaMashiach’ shine aihin suna Yesu Almasihu (Jesus)

Addinin krista a yanzu tatsuniya ce da daular Romawa na farko suka hada inji Ravaren Bempah.

Wani shahararren malamin addinin krista a kasar Ghana, Ravaren Isaac Owusu Bempah, shugaban cocin Glorious Word Power Ministry International ya kawo wani sabuwar fahimta a addinin krista.

A lokacin da Rev. Bempah yake hira da gidan talabijin din Kofi TV, ya ce Yesu Almasihu ba dan Allah ba ne kuma tsigar ‘Jesus’(Yesu) da ake kiran sa da shi jabu ne ba shi bane ainihin sunan sa. Bempah yace ainhin suna sa shine ‘Yeshua HaMashiach’ suna ‘Jesus’(YesuAlmasihu) Kage ne.

Bempah Raveren Bempha ya ce sunan Yeshua Hamashiach ya na nufin zaben Ubangiji, saboda haka ya na mamakin yadda aka yaudari kristocin duniya aka su, su ka dauki ‘Jesus’ (Yesu) a matsayin dan Allah kuma abun bauta a gare su.

Bempha yace tarihin Yesu Almasihu da muka karanta a takardun tarihi, da kuma sabuwar Injila tatsuniya ce da Daular Romawa na zamanin farko suka hada kuma suka mayar da shi addinin krista.

Duk lokacin da wani abun al’ajabi ya faru bayan Fastoci sun kira sunan ‘Jesus’ (Yesu Almasihu), ba sunan sa bane ke aiki ruhin Yeshua HaMashiach ke aiki saboda shine sanannen suna a samaniya, kuma dole masu imani dake duniya su yarda da wannan suna.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-11-13 — 12:12 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme