MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

GABA DA GABANTA: Sanata Dino Melaye Yaki Yarda Ya Shiga Asibitin Hukumar DSS Ya Kwanta A Kasa

                       Dino Melaye ya ki shiga asibtin DSS, ya kwanta a kasa

Hayaniyar sanata Dino Melaye da jami’an hukumar yan sanda bayan an daukeshi daga asibitin hukumar yan sanda zuwa asibitin hukumar leken asiri a DSS dake birnin tarayya Abuja.

Dan majalisan wanda ya kasance a hannun yan sanda tun makon da ya gabata da ya mika kansa ga hukumar ya ki shiga ginin hukumar DSS da akayi nufin shigar da shi domin yi masa jinya.

A maimakon haka, ya kwanta a kasa An tattaro cewa Sanatan ya tambaye jami’an tsaron shin ta wani dalili zasu kawoshi asibitin hukumar DSS.

Da suka ki fada masa, ya lashi takobin ba zai shiga asibitin ba,Dino Melaye ya ki shiga asibtin DSS, ya kwanta a kasa

Mun kawo muku rahoton cewa jami’an rundunar ‘yan sandan Nigeria (NPF) ta sake cafke Dino Melaye, sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta Yamma a majalisar dattijai ta kasa.

A ranar Juma’ar nan rahotanni suka bayyana cewa wasu da ba a san ko su waye ba, sanye da hular da ta boye fuskarsu, suka kutsa cikin asibitin rundunar ‘yan sanda dake Garki Abuja inda suka sace Melaye, wanda ke samun kulawar likitocin asibitin.

Yayinda hukumar yan sanda sukayi ikirarin cewa lafiyarsa kalau kuma zai iya gurfana a kotu, Sanata Dino Melaye ya jaddada cewa shi fa har yanzu bai da lafiya.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-12 — 11:56 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme