MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

GA FILI GA MAI DOKI:DUK WANDA YAYI YUNKURIN RUSA MIN GIDA SAI NA BASHI MAMAKI-Inji Sanata Deno Melaye

Mu Zuba Mu Gani: Duk Wanda Yayi Yunkurin Rusa Min Gida Zai Sha Mamaki-Inji Dino Melaye

Sanata Dino Melaye ya gargadi masu kokarin rusa gidan sa – A cewar Sanatan ya ji kishin-kishin din za ayi masa barna,Dino Melaye yace to yana jiran ya ga wanda zai taba ginin sa.

Da alamu duk wanda ya taba gidan Sanata Dino Melaye ba zai kwana lafiya ba kamar yadda Sanatan ya gargadi Gwamnatin Jihar Kogi kwanaki.

Dino Melaye zai ga bayan wanda ya taba masa gini Sanannen Sanatan nan na Najeriya Dino Melaye ya gargadi Gwamnatin Jihar Kogi game da yunkurin da yace ya ji ana yi na rusa gidan sa a Jihar.

 

Sanata Melaya yayi amfani da shafin sa na Tuwita yake cewa shege-ka-fasa! Sanata Dino Melaye na Jihar Kogi ya dade yana rikici da Gwamnan Jihar Yahaya Bello inda kwanaki yayi ikirarin an yi yunkurin kashe sa.

Sanatan wannan karo yayi wa Gwamnatin Jihar barazana game da shirin tana gine-gine sa.

Melaye ya ja kunnen Ma’aikatan Jihar da ke kula da harkokin gine-gine inda yace ya ji ana yunkurin rusa wasu gidajen sa da ke cikin Jihar da sunan gyara.

Updated: 2017-11-13 — 4:33 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme