MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

FATI WASHA NAKE SO KUMA ZAN IYA AURENTA-Inji Jarumi Nuhu Abdullahi

          FATI WASHA NAKE SO KUMA ZAN IYA AURENTA-Inji Jarumi Nuhu Abdullahi

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Jarumi Nuhu Abdullahi yana daga cikin jaruman da suka shigo Kannywood da kafar dama,duba da irin nasarorin daya ya samu a cikin dan kankanin lokaci.

A wata hira da jarumin yayi da jaridar Premium time ya bayyanawa duniya irin son da yake yiwa Fati Washa kuma har yayi furucin zai iya auren ta.

Acikin tambayoyin da gidan jaridar ke masa sun jefo  masa tambayar shin a masana’antar Kannywood,Wa yafi burgeka sai jarumin yace Fati Washa a koda yaushe itace zabina bazanyi nadama ba inma furta cewa ina sonta.

Jarumin ya kara da cewa ita din ta musamman ce,ta kasance tana kyautata min tabbas zan iya yin komai dan ganin nima na kyautata mata dan tana da saukin kai ga girmama manya.

Jaridar ta kara yi masa tambaya da cewa meyasa ka zabi Fati Washa ita kadai acikin duk ‘Yan matan Industry,Sai yace kamar yadda na gaya maka bazan iya bayyana maka yadda make jiba.

Amma ina matukar mutunta ta duk da ina da kawaye irin su Rahama Sadau da sauran su.

Dan Jaridar yace” Shin zaka iya aurenta?”

Sai Nuhu Yace”Tabbas in haka ta faru zanji dadi,in mutum ya kyautata maka zaifi kyau shima ka kyautata masa.”

Dan jaridar ya kara da cewa,shin Nuhu kana da burin aure nan kusa kuwa? Sai yace Gaskiya ba nan kusa ba dan har yanzu ni dan makaranta ne,sai na gama karatu na kafin na sanya maganar aure.

Ku Cigaba Da Kasancewa Da Dandalin Mujallarmu Don Samun Ingantatun Labarai Kai Tsaye Anan Gida Najeriya Hada Da Kasashen Ketare.

Daga Taskar Umar Mai Sanyi

Domin Kallon Sababbin fina finan Hausa Cikin sauka sai kuyi downloading App na Mujallarmu Tv a nan:
Download Mujallarmu TV (284 downloads)

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-06-12 — 1:12 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme