MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DUBA KAGA SHAHARARRUN ‘YAN WASAN KWALLON KAFA NA DUNIYA GUDA 10 DA REAL MADRID KE ZAWARCIN SU A WANNAN SHEKARA.

DUBA KAGA SHAHARARRUN ‘YAN WASAN KWALLON KAFA NA DUNIYA GUDA 10 DA REAL MADRID KE ZAWARCIN SU A WANNAN SHEKARA.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Kamar yadda muka sani dai Real Madrid tana daga cikin jerin manyan kungiyoyin kwallon kafa ta duniya,inda a take kan gaba wajen yawan  kofin duniya na champion league wanda a kakar bana  itace tayi nasara,inda yanzu haka tana da champion league har guda 13.

Shaharrarun yan kwallon duniya da dama suna ra;ayin taka leda a wannan kulob din ganin cewa kungiyar tana da kokarin gaske a fagen gwagwarmayar tamula da samun nasarori da dama.

Idan bamu manta dai a bayan nasarar da kulob din yayi a wannan shekarrar wajen lashe gasar champion a matakin karshe tsakanin su da kungiyar kwallon kafa ta Ingila wato Liverpool inda aka tashi da ci 3-1.

Sai dai kuma wasu bayanai sun biyo baya,inda ake saran tsohon mai horar da kungiyar wato Zinedine Zidine zai canza sheka zuwa wata kungiyar daban,duk da cewa bai fadi ra’ayin sa ba a fili.

Zidine zuwan sa Real Madrid yayi nasarar lashe kofin duniya na champion league har karo uku,inda yanzu yake ganin yakamata ace ya canza sheka zuwa wata kungiyar daban.

Buga da kari kuma shima shahararen dan wasan real madrid wato Cristiano ronaldo ana

tunanin cewa zai canza sheka zuwa tsohuwar kungiyar kwallon kafa daya fara  baro Manchester United a Ingila

Yanzu haka dai kungiyar ta Real Madrid ta shiga zawarcin manyan ‘yan wasa da zasu maye gurbin wadanda suke da muradin barin kungiyar.

Ga Sunayen ‘Yan Wasan Da Real Madrid Ke Zawarci kamar haka:-

1.Neymar

Daga Kulob din Parin saint German dake kasar faransa,akan farashin kasuwa Euro Miliyan 180 dan shekaru 25.

2.Robert Lewandowski

Daga kulob din Bayern Munchen dake kasar Germany,akan farashin kasuwa Euro Miliyan 90 dan shekara 29.

3.Christian Eriksen

Daga kulob din Totteham dake kasar Ingila,akan farashin kasuwa Euro miliyan 70 dan shekara 26

4.Eden Hazard

                      

Daga kulob din Chelsea dake kasar Ingila,akan farashin kasuwa Euro miliyan 100 dan shekara 27.

5.David De Gea

Daga kulob din Manchester United daake kasar Ingila,akan farashin kasuwa Euro miliyan 60 dan shekara

6.Paul Pogba

Daga kulob din Manchester United dake kasar Ingila,akan farashin kasuwa miliyan 90 dan shekara 25.

7.Harry Kane

Daga kulob din Totteham dake kasar Ingila,akan farashin kasuwa Euro miliyan 120 dan shekara 24.

8.Thibout Courtois

Daga kulob Chelsea dake kasar Ingila,akan farashin kasuwa Euro miliyan 60 dan shekara 25.

9.Dele Alli

Daga kulob din Totteham dake kasar Ingila,akan farashin kasuwa Euro miliyan 80 dan shekara 22.

10.Mauro Icardi

Daga kulob din Inter Milan dake kasar Italy,akan farashin kasuwa Euro miliyan 75 dan shekara 25.

 

 

Domin Kallon Sababbin fina finan Hausa Cikin sauka sai kuyi downloading App na Mujallarmu Tv a nan:
Download Mujallarmu TV (284 downloads)

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-06-12 — 1:02 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme