DAURE KARANTA KAJI: AYYUKAN AIKHARI 10 DA GADDAFI YAYIWA A’UMMAR KASAR LIBYA KAFIN A KASHE SHI

Karanta Kaji Ayyukan Alkhairi 10 Da Muhammad Gaddafi Yayiwa A’ummar Kasar Libya.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Kamar yadda muka sani marigayi Muhammad Gaddafi yayi gwagwarmaya da ‘yan ta’adda kamar yadda Sadam Husaini da Osama bin ladan sukayi lokacin da suke a raye.

Sai dai kuma Muhammad Gaddafi shugaban kasa ne a kasar Libya,wanda ya kawo sauye sauye da canji alokacin daya ke mulkin kasar,amma kuma daga baya sai aka samu wasu tsirarrun mutane dake masa kiyayya bisa ganin yadda yake taimakawa talakawa da ‘yan kasar ta Libya.

Kamar yadda muke da labari, bayanai sun nuna cewa an kashe Muhammad Gaddafi ne acikin kasar Libya ta hadin gwaiwar wasu azzulaman ‘yan siyasa saboda ganin yadda Muhammad Gaddafi ke kokarin kawo cigaba acikin kasar ta Libya.

Majiyar ta Dandalin Mujallarmu,ta samu kawo muku dalilin dayasa aka kashe Muhammad Gaddafi,ga dalilin kamar haka.

1- Alokacin mulkin gaddafi a kasar Libya kowa yana da cikakken ‘yanci na musamman a matsayinsa na dan kasa,tare da rabawa mutane gidaje kyauta ga’yan kasa da bakin haure.

2- Alokacin Mulkin Gaddafi Ilimi da hidimar asibiti idan an kwantar da majinyaci,ko bada magani kyauta ne.

3- Alokacin mulkin Gaddafi duk karshen wata ana baiwa ma’aikatan gwamnati kyautar kudade dalar Amurka N60’000,saboda suje su huta da iyalansu cikin walwala da nishadi.

4- Alokacin da Gaddafi ya amshi mulki a Libya suna fama da matsalar ruwan sha,amma da zuwan sa sai daya tabbatar da sun samu wadataccen ruwa sha kowane yanki na kasar.

5- Alokacin mulkin Gaddafi mutane da dama ‘yan kasar suna sha’awar noma da kiwo,amm da zuwan sa ya tanadar musu gidajen kiwo kaji da gonakin noma bila adadin kuma hakan duk a kyauta ne.

6- Alokacin mulkin Gaddafi idan mace ta haihu a gida ko asibiti za’a bata kyautar kudi dalar Amurka N5000,don taje da kula da kanta da jinjirinta.

7- Alokacin mulkin Gaddafi wutar lantarki kyauta 100%,sannan kuma farashin man fetur ya fadi warwas kusan kowa yana da karfin da zai iya saya yayi amfani dashi a gidan sa.

8- Alokacin da Gaddafi ya amshi mulki a Kasar Libya bashi ya dabaibaye ta,amma da zuwan sai da ya tabbatar babu wata kasa dake biyar kasar Libya bashi kona sisin kobo.

9- Alokacin da Gaddafi ya amshi mulki kashi 25%100 na ‘yan kasar Libya jahilai ne,amma da zuwan sa kashi 87%100 sun samu kammala karatun digiri a jami’o’i daban daban acikin kasar harda ketare.

10- Alokacin mulkin Gaddafi a kasar Libya idan aka saida danyen man fetur za’a turawa kowane dan kasa da kason sa zuwa asusun bankin ajiyar sa.

Wadannan sune kadan daga cikin dalilai goma na aikin kyautatawa da Gaddafi yayiwa Al’ummar kasar ta Libya,wanda ya janyo wasu azzalumai dora masa karan tsana babu gaira babu dalili,inda a karshe suka kulla masa wata munakisa ta hanyar raba shi da rayuwar sa kwata kwata a duniya.

ALLAH YA JIKIN GENENAL MUHAMMAD GADDAFI GWARZON SHUGABAN KASA MAI ADALCI DA KISHIN ADDININ MUSULUNCI…..AMEEM.

This website uses cookies.