MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DANDALIN KANNYWOOD:SHIGAR MATA SANA’AR FIM NADA MATUKAR MUHIMMACI-Inji Jaruma Maryam Sparkling

Shigar mata sana’ar fim na da matukar muhimmanci inji jaruma Maryam Sparkling

Maryam ta bayyana cewa ko shakka babu ita shigar ta masana’antar ta karu sosai da abubuwa daban daban duk da cewa bata dade sosai.

An haifi jarumar ne a garin Zaria ta jihar Kaduna inda kuma ta ce ta girma ne a na Zaria Daya daga cikin fitattun sababbin fuskoki a masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood mai suna Maryar Zaria da ake yi wa lakani da Maryar Sparkling ta bayyana cewa tabbas shigar mata a dama da su a harkar fim tana da matukar muhimmanci.

A yayin wata fira da tayi da majiyar mu, jaruma Maryam ta bayyana cewa ko shakka babu ita shigar ta masana’antar ta karu da muhimman abubuwa da dama wanda a da da bata shiga ba ba ta san su ba ko kadan.

Dandalin Mujallarmu  dai ta samu cewa an haifi jarumar ne a garin Zaria ta jihar Kaduna inda kuma ta ce ta girma ne a na Zaria da kuma jihar Katsina a wani lokaci a cikin rayuwar ta,Haka zalika jarumar ta labarta cewa tayi karatun Firamare da Sakandare duka a garin na Zaria kafin daga bisani ta je makarantar kimiyya da kere-kere ta garin Bida, jihar Neja inda ta kammala karatun Difuloma.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-05 — 10:56 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme