MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DANDALIN KANNYWOOD:KU KALLI YADDA JARUMA MARYAM BOOTH TA TAKA RAWA TA MUSAMMAN ACIKIN FIM DIN TURANCI NA KUDU

Ku Kalli Hotunan Jaruma Maryam Booth Tana shan Taba Acikin Fim Kudancin Najeriya. 

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Fitacciyar jaruma Maryam Booth kuma sananniya a masana’antar shirya fina finan hausa, ta taka tawa ta musamman acikin wani sabon fim data  fito aciki na kudu maisuna Sons Of Caliphates.

Fim din sons of caliphate fim ne na turanci  daya  kunshi  jaruman  kannwood da suka  hada da Yakubu Muhammad, Rahama sadau, da Maryam Booth.

Sai dai kuma ita  jaruma Maryam booth din ta taka rawa ta musamman, wanda sanadiyyyar haka ya janyo cecekuce  a tsakanin  masoyan  ta.

Kwanakin baya dai ne jarumar ta fito ta shaidawa masoyanta  cewa idan  sun daina  yawan  ganinta  a film sosai, ba laifin ta bane  laifin  daraktoci ne.

Inda a yanzu kuma jarumar ta karkata  akalarta  akan  fina finan kudu, da akeyi  da zalla harshen turanci  don ta sake baje basirar ta.

 

 

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-01-12 — 10:53 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme