MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DANDALIN KANNYWOOD: KASUWAR HAUSA FIM TA FADI WARWAS SABODA YAWAN HASKAWA A GIDAJEN KALLO NA SINIMA-Inji Kananan ‘Yan Kasuwa

Mun Daina Cinikin Kaset Sosai Saboda Yawan Haskawa A Gidajen Sinima-Inji Kananan ‘Yan Kasuwa.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Kamar yadda majiyarmu ta Dandalin Mujallarmu,keda labari daga cibiyar masana’antar fina finai ta kano da wasu kananan ‘yan kasuwa dake sana’ar saida kaset a garin kano da kewaye.

Su dai wadannan kananan ‘yan kasuwa sunyi korafi ne game da yadda kasuwar saida kaset ta canza akala a yanzu,sanadiyyar yawan haska fina fiani da akeyi a gidajen sinima kafin a saki a kasuwanni.

‘Yan kasuwan sunyi wanna kira ne a ranar alhamis 1 ga watan fabrairun shekarar nan,inda suka ce yanzu masoya kallon fina finan hausa sunfi son kallon fim a gidajen Sinima akan su saya a kasuwa,saboda ‘yan fim din suna halartar wajajen da ake nuna fina fina nan.

Kamar yadda wani karamin dan kasuwa maisuna Surajo Mukhtar ya shaidawa jaridar NAN,Surajo yace yanzu ana kwashe tsawon watanni ana haska fim daya a Sinima,inda karshe koda an sake sa akasuwa baya wata daraja tunda jama’a sun riga sun kalla tun a gidajen kallo na Sinima,Inji Shi.

A wani bangare kuma babban mai bada umarni kuma furodusa sannan kuma dan kasuwa darakta Falalu Dorayi ya bayyana dalilin dayasa ake haska fim a gidajen Sinima kafin a saki a kasuwa.

Falalu Dorayi yace dalilin dayasa yanzu ake haska fim a sinima shine,saboda sinima hanya ce data kawo cigaba a harkar fina finai ta duniya inda kusan ko ina a yanzu a duniya ana haska fim a sinima.

Falalu Dorayi ya kara da cewa sinima itace hanya da zata kawowa Furodusa kudinsa hankalin sa a kwance acikin dan ‘kan’kanin lokaci,ba kamar yadda idan an saki a kasuwa ba.inji shi.

 

 

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-02-07 — 11:37 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme