MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DANDALIN KANNYWOOD: JARUMA RAHMA SADAU TA FADA TARKON SOYAYYA DA WANI SAURAYI-Karanta Kaji

                       Jaruma Rahma Sadau Ta Fada Tarkon Soyayya

Marubuci: Haruna Sp Dansadau

Shahararriyar jarumar fina finan hausa Rahma sadau ta bayyanawa duniya irin zazzafar soyayyar da take yiwa saurayinta.

Majiyar ta Dandalin Mujallarmu ta samu labarin cewa jaruma Rahma Sadau ta kamu da soyayayr saurayinta sosai,makon dai daya gabata ne jarumar ta bayyana  wadannan hotunan  tana dariya baki har kunne  saboda zata sake ganin shi.

A wanna karon kuma Rahma ta fito ne ta dandalinta na sada zumunta inda ta futa wasu kalaman soyayya ga saurinyin  nata duk da cewa dai har yanzu bata bayyana sunan shi ba.

Ga Dai Abinda Ta Wallafa A Shafinta Kamar Haka-

“Its Funny How We Fall In Love With The Most Unexpected Person At The Most Unexpected Time.Regardless You Remain My Spark In The Dark”

Rahma ta rubuta cewa abin akwai ban mamaki irin yadda muke kamuwa da soyayyar wanda bamuyi tsammani ba,kuma a lokacin da bamuyi tsammani duk da haka kaine haskena acikin duhu.

“I May Not Be Able To Tell The World How Much I care,It Is A Language Only You Can Understand,Eternity Is The World For Us”

Ta kara da cewa ba lalle bane ta iya gayawa duniya irin soyayyar da take mishi ba,amma tasan cewa shi ya sani zasu kasance tare har abada.

A kwanakin baya ansha kishin kishin kan zargin cewa ko shahararriyar jarumar tana soyayya ne da shahararren jarumi Sadik Sani Sadik,amma har yanzu zargi bai tabbata ba amma yau da gobe watarana kome ke boye zai fito fili.

Fatan Mu Dai Allah Ya Bata Miji Nagari Abokin [email protected]

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-08 — 9:12 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme