MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DANDALIN KANNYWOOD: JARUMA RAHMA SADAU TA BAYYANA ALAKAR TA DA MAWAKIN AKON-Karanta Kaji

Dandalin Kannywood: Fitaccen Mawaki Akon Ya Taba Gayyata ta Zuwa Umrah Da Iyalan sa Amma Naki Amincewa Saboda Kaucewa Zargin Jama’a-Inji Rahma Sadau

Fitacciyar jarumar Kannywood Rahma sadau tayi tsokaci game da yadda jama’a suke ikirarin cewa tanada alaka ta soyayya tsakaninta da mawakin turanci na kasar Amurka Aliane Damala Bouga wanda akafi sani da Akon.

A tattaunawar da akayi da ita a wani shirin kundin Kannywood da tashar arewa 24 da take shiryawa akowace ranar talata da Aminu sharif momoh ke gabatarwa jarumar tace.

” Bata taba tsamanin zata hadu da mawakin turanci Akon ido da ido ba,saboda tsawon shekaru tana jin wakokinsa sannan kuma shin fitaccen mawaki ne da duniya ta san shi wanda yayi suna sosai,saboda haka yasa tayi matukar farincikin da gayyatar da yayi mta kuma ta amsa gayyatar.inji Rahma sadau.”

Jarumar ta kara da cewa jama’a sunta rade radin cewa¬† mawakin ya nemi data canja addini zuwa addinin kirsitanci,jarumar tace toh hakan ba gaskiya bane domin duk wanda yayi mu’amula da mawaki Akon bazai fadi haka ba,saboda shi musulmi ne kuma yana da matan aure uku.

Har ila yau jarumar tace tasamu cikakken labarin mawakin inda mutane da dama suka jaddada mata  cewa aduk watan ramadan mawakin yakan kebe kansa daga mutane saboda ya samu damar gudanar da ibadar sa cikin kwanciyar hankali,inji Rahma sadau.

Akarshe jarumar ta bayyana cewa mawakin ya taba gayyatar ta zuwa Umrah tare da iyalan sa amma taki amincewa saboda kaucewa zargin jama’a da kuma gudun abinda zai iya zuwa ya dawo daga wasu tsirarrun mutane.

Bugu da kari jarumar tayiwa masoyanta albishir da sabon fim dinta maisuna”MATI A ZAZZAU” wanda zai fito nan bada jimawa ba.

 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-12-03 — 11:43 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme