MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DANDALIN KANNYWOOD: Jaruma Kuma Uwa A Masana’antar Hausa Fim Ta Bayyana Shugaba Buhari Matsayin Dan Takararta

Dandalin Kannywood: Hajara Usman ta fadi wa zata zaba a matsayin shugaban kasa

Fitacciyyar jaruma kuma daya daga cikin iyaye a masana’antar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood watau Hajara Usman ta bayyana wanda zata goyawa baya a zaben gama gari na shekarar nan ta 2019 a matsayin shugaban kasa.

Jarumar dai ta bayyana cewa in Allah ya yarda zata yi aiki tare domin samun nasarar Shugaba Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa kamar yadda dayawa daga cikin jaruman masana’antar.

“Ba zai yiwu a ce dukkaninmu, kowa da kowa sunansa yana cikin jadawalin sunayen masu gudanar da yakin neman zaben jam’iyyar APC ba.

“Amma in sha Allahu dukkaninmu za mu yi aiki tare domin samun nasarar Shugaba Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa, kuma a tare za mu yi bikin samun nasara idan Allah ya yarda”, tace.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gayyaci wasu daga cikin jaruman Kannywood ciki hadda ita Hajara Usman din a fadar sa inda ya jinjina masu kan goyon bayan da suke nuna masa.

 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-10 — 10:29 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme